Ba wanda ya dakatar da ni - Rahama Sadau

Ba wanda ya dakatar da ni - Rahama Sadau

Rahama Sadau ta shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa ba bu wanda ya dakatar da ita daga fina-finan Hausa, inda ta ce ita ma ta ji ana fadar batun dakatarwar ne kawai a kafafen yada labari.

A bara ne kungiyar masu shirya fina-finai ta ce ta dakatar da Rahma bayan da aka zargeta da rungumar wani mawaki a lokacin da ta fito a wata waka.

Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a masana'antar Kannywood, abin da ya sa daga bisani jarumar ta bai wa magoya bayanta hakuri.

Sai dai BBC ta fahimci cewa jarumar ba ta sake yin wani fim ba tun bayan sanar da dakatar da ita.

Hatta fim din Rariya da ta fito a ciki kwanan nan, an yi shi ne kafin batun dakatarwar da aka ce an yi mata.