Hotunan abin da ya faru a Afirka a makon jiya

Wasu zababbun hotuna abubuwan da suka faru a sassa daban-daban na nahiyar Afirka a makon jiya.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A ranar Juma'a masu abin hawa sun fuskanci matsaloli sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a Abidjan babban birnin Ivory Coast
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar ne dai aka rantsar da alkalan kotun hukunta manyan laifuka ta musamman a birnin Bangui. Aikinsu shi ne su gudanar da bincike da kuma ladabtar da masu take hakkin dan Adam da laifuykan yaki a jamhuriyar Tsakiyar Afirka tun daga shekarar 2003.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yar Kamaru Dongmo Auriole yayin da za ta wulwula kwallo karo na uku a gasar mata ta wulwula kwallon ranar Talata a kasar Hungary.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani mai karbar haraji dan kasar Laberiya ya rike takardar da ke magana kam ranar biyan haraji, inda yake kokarin nuna muhimmanci biyan kudin haraji wajen dorewar ayyukan ci gaba, a ranar Asabar.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mambobin wata runduna ta musamman a gabashin Libya, suka dauki hoton kansu kafin su 'kwato' birnin Benghazi da ke gabashin kasar ranar Labara, bayan da aka shafe shekaru ana yaki da masu tada kayar baya.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mambobin rundunar tsaron Tunisiya yayin da suke zanga-zanga a kusa da fadar majalisar kasar ranar Alhamis, inda suke nuna goyon bayansu ga dokar kare su daga hare-haren da suke fuskanta idan suna bakin aiki.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mai zanga-zanga dauke da rubutun da yake nuna cewa ba ya goyon bayan sauya kundin tsarin mulkin kasar Mali, a birnin Bamako ranar Asabar, sun fito kan titi ne don nuna adawarsu kan batun, masu suka sun ce gyara kundin tsarin mulkin zai ba wa shugaban kasar damar samun karfin mulki.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Har ila yau a birnin Bamako, Shugaban Kasar Chadi Idriss Deby (daga hagu) yana ganawa da takwaransa na Faransa Emanuel Macron yayin babban taro kan yankin Sahel ranar Lahadi.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wadansu kayayyaki da aka baje kolinsu a kan wata mota da aka ajiye a unguwar Ikeja da ke jihar Legas a Najeriya ranar Talata.