Ra'ayi: Me ka fahimta da sake fasalin Najeriya?
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi: Me ka fahimta da sake fasalin Najeriya?

A Najeriya ana ta tabka muhawara a kan yadda ake mulki da kuma tsarin zaman tarayyar kasar. Yayin da wasu ke cewa ya kamata a sake lale, a sake fasalin ikon gwamnatin tarayyar da na jihohi, wasu kuma suna cewa ne ba su ga aibin tsarin da ake da shi yanzu ba, bare har a ce a sake shi. Me ya jawo wadannan kiraye-kiraye? Kuma ya kamata a sake fasalin yadda tarayyar kasar take ko a'a? Batun da aka tattauna akan shi kenan a filin Ra'ayi Riga.