Ko wane irin aiki ne ke gaban INEC?

hukumar za ta ci gaba da sabunta katocin zabe ga 'yan kasar
Image caption Jami'an hukumar zaben Najeriya

Farfesa Mahmood Yakubu,shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya, ya rantsar da sabbin kwamishinonin hukumar na jihohi su 14.

Kowanne daga cikin su zai yi wa'adin shekara biyar wanda za a iya sabunta wa.

Jinkirin da aka samu game da na da sabbin kwamishinonin dai bai shafi lamuren zabubukan da aka gudanar ba kamar yadda shugaban hukumar ya sanar.

Domin hukumar tana da kwararrun ma'aikata na dun-dun-dun da ke gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Tuni dai hukumar ta soma gudanar da aikin sabunta katocin zabe ga wadanda suka batar da nasu ko kuma suka lalace sanadiyar rikice-rikice.

Hukumar zaben za ta ci gaba da sabunta katuna ga jama'a tun har zuwa lokacin babban zabe na kasa baki daya.

Labarai masu alaka