Za a gwada lafiyar Lukaku a Man United

Pogba da Lukaku Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta yi gwajin lafiyar Romelu Lukaku bayan ta kammala cinikinsa a kan fam miliyan 75 daga Everton.

Man U ta bayyana cewa tana farin ciki da sayen dan wasan kuma za a kammala kulla yarjeniyar ne bayan gwajin lafiyar dan wasan mai shekara 24 da haihuwa.

A da ana ganin Lukaku zai koma tsohuwar kungiyarsa ta Chelsea ne, wacce ya je daga Anderlecht a shekarar 2011.

Man Utd ta amince ta sayi Lukaku fan miliyan 75

Lukaku ya yi watsi da makudan kudaden Everton

Kwarewar Lukaku ya wuce zama a Everton — Koeman

Kocin Manchester United Jose Mourinho ne ya sayar da dan wasan gaban a kan fam miliyan 28 ga Everton a lokacin yana kocin Chelsea a karo na biyu a shekarar 2014.

Dan wasan dan asalin kasar Belgium ya zura kwallo 25 a gasar Firimiyar da aka kammala.

Tawagar ta Jose Mourinho na fatan kammala cinikin dan wasan kafin kungiyar ta tafi Amurka domin atisayi ranar Lahadi.

Labarai masu alaka