Nigeria: An sasanta sabanin masarautar Sokoto

Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar Hakkin mallakar hoto Getty Images

An cimma sulhu a sabanin da ya kunno kai tsakanin Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar III da daya daga cikin manyan 'yan majalisarsa, wato Magajin garin Sakkwato Alhaji Hassan Danbaba.

Zaman ya biyo bayan kwashe kwanaki da wasu manyan sarakunan arewacin Najeriya suka yi suna kokarin sasanta manyan sarakan biyu.

Sulhun ya kai zangon karshe ne ranar Asabar da wani zaman da aka yi a birnin Sakkwato.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu yana daya daga cikin manyan sarakuna biyu da suka jagoranci wannan sulhun wadanda ya hada da Sarkin Gwandu.

"Mun kawo shi wajen mai alfarma sarkin Musulmi ya tuba ya ba shi hakuri; mai alfarma ya karbi wannan ya yafe masa, wannan magana ta wuce," in ji sarkin Kano a wata hira da ya yi da BBC.

A ranar Litinin ne da magajin garin wanda shi ne mutun na uku mafi girman mukami a majalisar sarkin Musulmi ya fice a fusace daga wani zaure da suke ganawa da Sarkin.

Daga bisani kuma ya sanar da yin murabus daga kan mukaminsa wanda yake rike da shi tsawon shekaru 20.

Magajin garin dai ya yi zargin cewa sarkin ya ci masa zarafi a wajen wani sulhu da ake tsakaninsa da wani da sarkin ke son bai wa wata sarauta.

Sai dai masarautar ta ce ya yi hakan ne saboda sarkin ya ki amincewa ya sa baki kan wata matsala da ke tsakanin kamfaninsa da Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati (EFCC).

Labarai masu alaka