'Mu rika ba marasa galihu tsofaffin littattafai'

Littafan karatu Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Yana da muhimmanci a rika tattara littafan da aka gama amfani da su don taimaka wa marasa galihu

A Najeriya, wasu matasa sun kafa wata kungiya domin tara litattafan karatu da aka fi sani da 'Text Books' da aka riga aka gama amfani da su, suna kai wa makarantun gwamnati da na marasa galihu.

Kungiyar mai suna 'Book Bank' ta ce hakan zai taimaka matuka wajen inganta ilmi a tsakanin yara marasa galihu.

An kafa kungiyar ne ta Book Bank a shekarar 2016, kuma tana gudanar da ayyukanta ne a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya da kuma Lagos.

Sa'id Saidu Malami shine shugaban kungiyar ta Book Bank da ya shaida wa BBC cewa babu amfani mutane su tara litafai da yawa tun daga na makarantun naziri, firamare da na sakandare a jibge a dakunan ajiya a gidaje har su lalace.

''Abokina ya bani shawara mu rika tara litafan mu rika kai wa wadanda suke so, amma sai na ce gara mu kafa kungiya ta yadda za mu iya jan hankulan jama'a suna bayar da gudumawa''.

Malam Sa'idun ya kuma ce su kan yi amfani da shafukan sada zumunta kamar su Twitter da Facebook wajen kira ga jama'a tare da wayar musu da kai sun rika tara litafan da suka gama amfani da su don a rika tallafawa yara marasa galihu a makarantu.

'' Idan mun kai makarantun yaran suna nuna farin cikinsu, hakan na kara mana karfin guiwa''.

Wata matashiya Rukayya Bobboi, wacce ita ma da ta kai wa wannan kungiya ta Book Bank gudumawar litafai guda 50, ta bayyana muhimmancin yin hakan.

''Yara suna son takardu, idan ka je za ka ga idan ba su da litafin karatu ba sa jin dadi a makarantu,'' a koda yaushe zan rika kawo wa in dai ana taron tattara litafan''.

Labarai masu alaka