Abin da ya sa ake gasgata batun 'shinkafar roba'

Small pile of long grain white rice over a wooden surface Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Shinkafar robar' tana kama sosai da sahihiyar shinkafa

Duk da cewa babu manyan hujjojin da ke nuna cewa akwai "shinkafar roba" a kasuwa a wasu kasashen Afirka, amma kafafen sada zumunta suna bayyana cewa hakan na faruwa.

Akwai labarai da kuma hotunan bidiyo da ke nuna "shinkafar robar" a shafukan sada zumunta.

A watan Disambar bara ne aka yada labarin "shinkafar robar" a Najeriya.

Amma sai a makonnin da suka wuce ne jitar-jitar ta bulla kasashen Senegal da Gambia da kuma Ghana wadda har sai da ta kai jami'an kula da abinci na kasar kaddamar da bincike game da batun 'shinkafar robar.'

An bukaci 'yan kasuwa da masu amfani da shinkafa da su mika samfurin shinkafar da suke zargin ta roba ce ga jami'an - wanda kuma a karshe suka tabbatar da cewa babu shinkafar robar a kasuwannin Ghana.

An fara yada jitar-jitar shinkafar robar ne a shekarar 2010 a kafofin sada zumunta, inda ake cewa kasar China ce take samar da ita.

Daga nana ne ake ta baza jita-jitar har cikin shekarar 2016, inda jami'an hukumar kwastam na Najeriya suka cafke tan 2.5 na shinkafa, kamar yadda suka bayyana.

'Ana gudanar da bincike kan shinkafar roba'

Nigeria: Kwastam ta kama shinkafar roba

Menene gaskiya kan shigar da 'shinkafar roba' Nigeria?

Jami'an sun yi ikirarin cewa shinkafar da suka kama "ta roba ce", sai dai daga bisani sun ce "ba ta roba ba ce", bayan da ministan ciwon lafiyar kasar ya ce babu hujjar da nuna akwai shinkafar roba a kasar.

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar ta ce gwajin da ta yi ya nuna cewa shinkafar da ake zargin ta roba ce ba ta kunshi kwayoyin Bacteria masu yawa ba.

Amma sai aka ci gaba da yada jita-jitar cewa ana sayar da roba a matsayin shinkafa.

Akwai hotunan bidiyo da suka rika ruruta batun ta hanyar nuna wani abu mai kama da shinkafar roba.

Har ila yau, akwai wadanda ma suke nuna yadda ake kera shinkafar a masana'antu.

Alexander Waugh shi ne daraktan kungiyar masu noman shinkafa ya ce hotunan bidiyon suna iya kasancewa sahihai ne - "amma ba ina nufin shinkafa ta roba ce ba. Idan aka sarrafa shinkafa yadda ya dace to za ka ga tana sheki kamar roba," kamar yadda ya bayyanawa BBC.

Hakazalika, dan jaridar Faransa Alexandre Capron wanda yake nazari kan batun, ya ce wasu mutane suna yada hotunan da ke nuna "shinkafar robar" ne don kawai masu cin shinkafa su kauracewa shinkafar kasashen waje, su koma cin wadda ake nomawa a gida.

Ya ce: "Jita-jitar shinkafar robar ta fi yin karfi a kasashen da suka dogara da shinkafar waje kamar Kwaddibuwa da Senegal. Batun ya yi karfin da sai da gwamnati ta fitar da sanarwa... kan abin da ya jawo shinkafar robar."

Hassan Arouni na nan BBC wanda shi ma ya yi nazari kan shinkafar robar ya ce ba zai iya gane cewa ko mutanen Afirka ta Yamma suna yada jitar-jitar ne saboda kasashen da suke shigo musu da abinci kamar China.

Kodayake, ya ce yana ganin bai dace jami'an kula da lafiyar abinci a kasashen Yammacin Afirka su tunkari batun kai-tsaye ba.

Ya abin da yakama su yi shi ne "su fito fili su cewa jama'a batun shinkafar roba ba gaskiya ba ne. Hakan ne zai sa mutane su game cewa batun labarin kanzon-kurege ne wanda wani kawai ya kirkira don ya wallafa a Intanet," in ji Arouni.

Labarai masu alaka