Nigeria: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum '15' a Suleja

Ambaliyar ruwa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana danganta rashin samar da hanyoyin ruwa yadda ya kamata da babban dalilin da yake jawo ambaliyar ruwa a kasar

Akalla mutum 15 ne suka mutu bayan saukar wani ruwan sama a unguwar Kaduna-Road kusa da Abuja a Najeriya, kamar yadda wani ganau ya shaidawa BBC.

Alhassan Danbaba ya ce gadoji da gidaje fiye da talatin ne ambaliyar ruwan ta yi gaba da su, na yankin karamar hukumar Suleja mai makwabtaka da birnin Abuja.

Ya kuma ce wannan ita ce ambaliyar ruwa mafi muni da suka taba fusknata a yankin cikin shekaru da dama.

''Amma gaskiya matsalar ita ce mutane na gina gidaje a bakin ruwa ko kuma ma hanyar da ruwa kan bi'', shi yasa a ko wace damuna akan samu wannan matsala.''

Shima wani mazaunin yankin Dahiru Adamu ya bayyana yadda lamarin ya faru;

"An fara ruwan saman ne tun daren Asabar da misalin karfe 11 na dare har zuwa wayewar gari . Daga nan ne sai ambaliyar ruwan ta fara gadan-gadan a unguwar Hayin Nasarawa,"

Ya ci gaba da cewa "Ruwan ya ci motoci da gidaje da dama, kuma akalla mutum shida sun rigaya sun mutu. Kuma mun yi asarar dukiya mai yawa daga wannan amabaliyar ruwan."

Kokarin jin ta bakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ya ci tura don ba su amsa kiran da muka yi musu ta waya ba.

Labarai masu alaka