Ambaliyar ruwa ta tsayar da al'amura a Lagos

Ambaliyar ruwa Hakkin mallakar hoto Getty Images

Al'amura sun tsaya cak, yayin da mutane suka kasance a gida a wasu sassan birnin Legas da ke kudancin Najeriya, bayan wani ruwansa da aka kwashe kwanaki ana yi ya haddasa ambaliyar ruwa.

Mazauna unguwannin Lekki da Victoria Island sun wari gari ranar Asabar da ambaliyar ruwa bayan kwashe kwana biyar a ruwa, kamar yadda wata wadda take zaune a Legas ta shaida wa BBC.

"Yau kwana biyar ke nan ana ruwa babu dauke wa a unguwar Lekki. Ko 'ya'yanmu ma a cikin ruwa suke zuwa makaranta cikinsa suke dawowa," in ji ta.

Har ila yau, wata ganau ta shaidawa BBC cewa: "Ruwa marka-marka ake yi a nan Legas wanda kuma hakan ya sa mu da yaranmu mun kamu da mura."

An sace 'yan makaranta shida a Legas

Kwastam ta kama makaman yaƙi a Legas

Kotu ta bai wa gwamnati kudin da aka gano a Legas

Kodayake babu rahotan da ke cewa an samu asarar rai, amma mazauna yankin da abin ya faru sun ce sun tafka mummunar asara.

Ruwan ya rika shiga cikin gidajen jama'a yayin da a wasu unguwannin ambaliyar ta tilasta wa jama'a fara amfani da kwale-kwale don yin zirga-zirga.

Hakazalika, ambaliyar ta jawo dauke wutar lantarki a wani bangare na birnin saboda yadda falwayoyin wutar lantarki suka fadi.

Ana danganta rashin samar da hanyoyin ruwa yadda ya kamata da babban dalilin da yake jawo ambaliyar ruwa a birnin.

Labarai masu alaka