Bidiyo ya nuna yadda Boko Haram ta harbe mutum takwas

Abubakar Shekau
Image caption Abubakar Shekau ya ce ba za su daina yaki da gwamnatocin 'kafirai' ba

Mayakan kungiyar Boko Haram sun fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna suka harbe mutum takwas a wasu kauyuka.

Kamfanin dillacin labarai na AFP ya ce ya samu bidiyon wanda ya nuna yadda mayaka hudu suka kwantar da mutanen bayan sun rufe musu fuska sannan suka harbe su.

AFP ya ce mutanen da ke wurin sun yi ta sowa lokacin da ake hudu kauyawan.

A cewar Boko Haram, mutanen suna adawa da matakin da kungiyar ta dauka na jaddada dokokin addinin Musulinci.

BBC ba ta tabbatar da ingancin bidiyon ba, amma a baya AFP ya sha wallafa ingantattun faya-fayen bidiyon mayakan.

Wani mutum da ke sanye da rawani kuma ya shaida wa taron mutanen cewa wadanda aka harbe sun yi ridda, in ji AFP.

"Mutanen da aka harbe ba su da bambanci da 'yan kato-da-gorar da suke yakarmu, wadanda ke yin leken asiri a kanmu da kuma sojojin Najeriya", a cewar mutumin.

Bidiyon ya nuna shi yana gargadin wadanda ke wurin cewa za a harbe su kamar yadda aka yi wa 'yan uwansu idan suka saba wa dokokin kungiyar.

Idan wannan bidiyo ya tabbata, to zai iya nuna cewa har yanzu akwai wasu yankuna da ke karkashin ikon kungiyar, sabanin ikirarin da mahukunta musamman a Najeriya ke yi na akasin haka.

Sai dai ba a bayyana wuri ko kuma lokacin da aka nadi wannan bidiyo ba.

Boko Haram, wacce ke kokarin kafa daular Musulunci, ta rasa mafiya yawan wuraren da ta mamaye a baya ga sojojin Najeriya.

Labarai masu alaka