Afirka ta Kudu: Zaki hudu sun tsere daga a gandun daji

Zaki Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana fargabar cewa zakokin ka iya farmaki kan garken dabbobi a kusa da kauyen Matsulu

Masu lura da gandun daji a Afirka ta Kudu na can su na neman wasu zakoki hudu da suka gudu daga gandun dajin kasar.

A wata sanarwa da ta fitar, hukumar gandun dajin Afirka ta Kudun ta ce a daren Lahadi ne zakokin suka tsere daga gandun dajin na Kruger, kuma an yi musu ganin karshe a kauyen Matsulu.

Ta kuma gargadi mazauna yankin da su yi ''taka-tsan-tsan''.

Babu wani tabbaci kan yadda zakokin suka tsere daga gandun dajin da aka riga aka kewaye.

Gandun dajin na Kruger na daya daga cikin manyan wuraren ajiyar dabbobi a Afirka .

Hakan dai na zuwa ne bayan da a cikin watan Mayu wasu zakokin guda biyar suka tsere daga wannan gandun daji.

Amma daga bisani an sake cafke hudu, sai dai har yanzu na biyar din babu labarinsa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Taswirar Afirka ta Kudu

Labarai masu alaka