India: Ya kashe matarsa saboda lattin kin dafa abincin dare

Kunshi
Image caption Cin zarafin mata a gidajen aure ya zama ruwan dare a kasar India,

'Yan sanda a kasar India sun ce sun cafke wani dattijo mai shekara 60 da ya hallaka matarsa ta hanyar bindigewa saboda bata gama abincin dare da wuri ba.

A daren Asabar ne Ashok Kumar ya dawo gida cikin maye, inda gardama ta kaure tsakaninsa da matarsa , kamar yadda wani babban jami'in 'yan sanda Rupesh Singh ya shaida wa BBC a birnin Ghaziabad da ke kusa da Delhi babban birnin kasar.

An garzaya da Sunaina, mai shekara 55 zuwa asibiti bayan da ta samu rauni daga harbin bindigar da ta samu a ka, amma kafin a isa asibiti rai ya yi halinsa.

Mr Kumar ya amsa laifin da ya aikata, kuma yanzu haka yana cikin nadama, in ji Mr Singh.

" Mutumin ( Mr Kumar) ya saba shaye-shaye a kullum. A ranar Asabar ya dawo gida a buge, inda ya fara sa-in-sa da matarsa. Ta cika da bacin rai game da dabi'arsa, tana so ta yi masa magana a kai, amma ya bukaci ta kawo masa abinci da wurwuri,'' in ji Mr Singh.

Ya kara da cewa '' Ya fusata da bata lokacin da ta yi kawai sai ya harbe ta''.

Wakiliyar BBC a birnin Delhi ta ce irin wannan cin zarafi da mata ke fuskanta a gidajen aurensu ba sabon abu bane a kasar ta India- yana faruwa a ko ina a fadin duniya- amma abinda ya banbanta India da sauran kasashe shine dabi'ar rashin fitowa fili a bayyana.

Labarai masu alaka