Kun san dalilin da ya sa adadin 'yan Nigeria zai karu?

TSARIN IYALI Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana fatan samar da tallafi ga kasashe masu tasowa domin kula da tsarin kayyade iyali

Hukumar majalisar dinkin duniya mai kulla da iyali, da gidauniyar Bill da Melinda Gates da asusun tallafi don bunkasa kasashen waje ta Burtaniya sun shirya taro kan tsarin iyali a birnin London.

Sai dai kuma wannan taro na zuwa ne a daidai lokacin da ake hasashen cewa Najeriya za ta kasance kasa ta uku a duniya wajen yawan al'umma zuwa shekara ta 2050 bayan kasar China da India.

A yayin da ake shirin bude taron kolin na duniya game da tsarin iyali a London din, akwai babban kashedi da ya saka likitoci a cikin wani yanayi na su yi zabi mai wuyar dauka.

Ko dai kasashe masu halarta taron su amince da taimakon da suke samu ta bangaren yaki da cututtuka kamar su AIDS wato SIDA, su kuma kama bakin su yi shiru game da maganar zubar da ciki, idan ba haka ba kuma su manta da maganar samun tallafi daga manyan masu bayar da taimako na duniya .

Wannan na daga cikin ka'idojoin da aka tsara a Mexico kan manufofin da kasashen duniya za su runguma da hannnu biyu da shugaban Amurka zai yi amfani da su kan maganar zubar da ciki, da kuma yanzu suka hada da maganar dimbin bilyoyin kudin agaji da Amurka ta ware wajen taimaka wa kasashen duniya yakar cutar sida.

Wannan zabi dai abu ne mai wuya , wanda ya kasance ga koshi ga kwanan yunwa, musamman ga kasa kamar Afirka ta kudu da ke kunshe da mutanan mafi yawa na duniya da ke dauke da cutar AIDS.

Yanzu haka an kiyasta cewa al'ummar kasar ta Afirka ta kudu da ke dauke da wannan larura sun kai milyan bakwai.

To sai dai kuma ba kasar Afirka ta kudu ce kawai ba ke faduwar gaba ba game da lamarin, hatta a sauran kasashen Afirka wannan wata babbar damuwa ce.

Gama da wannan lamari a kasa kamar Najeriya, an sanar da cewa mutane miliyan daya da ke dauke da cutar AIDS za su mutu a cikin shekaru biyar masu zuwa, muddin gwamnatin kasar ba ta dauki matakan shayar da su magungunan kyauta game da cutar ba.

A halin yanzu 'yan Najeriya kimanin milyan daya ne ake wa magani game da cutar ta aids .

Labarai masu alaka