Za a fatattaki miyagu daga gwamnatin Buhari — Aisha

Uwargidan Shugaban Najeriya Aisha Buhari Hakkin mallakar hoto Aisha Buhari Twitter
Image caption A yanzu haka Aisha Buhari tana London domin duba mijinta

Uwargidan Shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta yi wani shagube kan al'amuran da suke faruwa a gwamnatin mijinta, tun bayan tafiyarsa jinya karo na biyu a birnin London.

Ta wallafa shaguben ne a shafinta na Facebook ranar Litinin, inda ta yi amfani da abin da Sanata Shehu Sani na jihar Kaduna ya rubuta yana habaici ga wasu 'yan siyasar kasar.

A makon da ya gabata ne Aisha Buhari ta sake komawa London domin duba Shugaba Muhammadu Buhari, mai shekara 74, wanda ya shafe sama da wata biyu a can yana jinya.

Kawo yanzu dai babu wanda ya san cutar da ke damunsa, kuma ba a ganshi a bainar jama'a ba tun bayan tafiyar tasa.


Abin da Sanata Shehu Sani ya wallafa

"Tuni aka daina yi wa babban zaki addu'a, har sai ya dawo sannan za ka ga suna rawar jikin kasancewa a layin farko na 'yan kanzagi.

A yanzu kuraye da dila na ta yi wa juna rada suna kokwanton ko Sarki Zaki zai dawo ko a'a. Sarkin dai bacci yake yanzu kuma ba mai iya tabbatar da cewa zai ta shi ko ba zai tashi ba.

Amma fatan kuraye da dila shi ne kar ya tashi don su samu su zama sarakuna. A gefe guda kuwa sauran kananan dabbobi (talakawa) na ta addu'a Sarki Zaki ya dawo don ya ceci dawa daga mugayen namun daji irin su kuraye da diloli."

Amsar da Aisha Buhari ta bayar:

"Allah ya amsa addu'ar kananan dabbobi (wato talakawa), nan ba da dadewa ba za a fatattaki kuraye da dila daga dawa.

"Mun matukar yarda da addu'a da goyon bayan kananan dabbobi (talakawa).

"Allah ya ja zamanin talakawa, Allah ya ja zamanin Najeriya."


Wadannan maganganu na Aisha Buhari sun janyo sharhi da ka-ce na-ce sosai a kasar, musamman a shafukan sada zumunta da muhawara.

Hakkin mallakar hoto Halima Umar
Image caption Jam'iyyar PDP ma ta wallafa a Twitter cewa 'yan Najeriya su fahimci Aisha Buhari ta kira su dabbobi marasa karfi
Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Wasu kuwa ba su ga laifi a maganganun nata ba don a cewar su kamar 'karin magana ce'.

Kuma ga alama kalaman nata sun nuna cewa batun da aka dade ana yi cewa 'yan fadi-tashi da gogayyar neman mulki a fadar gwamnatin Buharin suna hana ruwa gudu.

An yi ta mayar da martani a shafukan inda wasu ke jinjinawa kalaman nata, yayin da wasu kuwa ke sukarta da cewa ta aibata 'yan Najeriya da ta kira su da dabbobi marasa karfi.

Wani mai sharhi kan al'amuran siyasa Bashir Baba, ya shaida wa BBC abin da ya fahimta da wannan shagube na Aisha Buhari, "Ni abin da na fahimta shi ne tana son nunawa 'yan Najeriya cewa, abin da ake fada na zuzuta halin da Shugaba Buhari ke ciki ba haka yake ba.

"So take ta nuna cewa mijinta ya kusa ya warware ya dawo gida. Tana nuna cewa Buhari yana samun sauki, kuma yana gab da dawowa ya wancakalar da wasu miyagu da suka addabi gwamnatinsa."

A cewar Bashir Baba, wadannan maganuganu na Aisha Buhari na tabbatar da batun da ta taba yi a wata hirarta da BBC a baya, inda take cewa wasu tsiraru sun mamaye gwamnatin suna hana ruwa gudu.

"Dama ba gwamnatin da ba a samun 'yan fadi-tashi da gogayyar neman mulki duk duniyar nan.

"Ba shakka ta ga yanayin jikin mijinta yana samun sauki ne shi ya sa ta zo take gargadin miyagun da suka addabi wannan gwamnatin don su shiga taitayinsu. Mu kuma talakawa da muke gefe guda muna shirin ganin buduri kenan.

To sai dai wanne irin buduri ne zai faru idan shugaban ya dawo?

Sai Bashir Baba ya ce: "Tabbasa za a yi buduri don kuwa zai dauki matakai a kan miyagun nan da suka dinga tsula tsiyarsu a yayin da baya nan. Ai shi ne ma makasudin sakon ita Hajiya AIsha."

Hakkin mallakar hoto Twitter

A cewar Bashir Baba, tun bayan hirar da AIsha Buhari ta yi da BBC a bara inda ta koka kan yada al'amuran gwamnatinsa ke tafiya sai abubuwa suka fara daidaita., hakan na nufin batun nata ya yi tasiri kwarai da gaske.

A yanzu haka dai Aisha Buhari tana Birtaniya don duba mijinta da ya shafe kwana 64 yana jinyar rashin lafiyar da ba a san mece ce ba.

Labarai masu alaka