'Yadda na kusa auren 'yata saboda yawan 'ya'yana'

Ghana yara Hakkin mallakar hoto Getty Images

Game da batun tsara iyalin, yin aure da kuma tara 'ya'ya abubuwa ne da ake yi wa kallon masu sauya rayuwar ko wanne bil'adama.

Kofi Asilenu a Ghana yana ganin ya fada cikin wannan rukuni da rayuwarsu ta sauya sakamakon haihuwar 'ya'ya, domin kuwa 'ya'yansa dari daya cif! Kuma a cikin wata hira da wakilin BBC a Ghana Thomas Naadi ya fada masa cewa yana fatan kara samun wasu 'ya'yan.

Kauyen Amankrom na da nisan tafiyar mintoci 45 a mota daga Accra, babban birnin kasar Ghana. Mazauna kauyen ba su wuce mutum 600 ba, kuma a nan Kofi Asilenu mai shekaru 80 a duniya kuma mai 'ya'ya fiye da 100 yake da zama.

Yawan Iyalinsa ne kashi daya bisa uku na al'ummar da ke kauyen.

Haihuwar yara da yawa ba wani sabon abu ba ne a wuraren da ake da iyalai masu yawa a fadin nahiyar Afrika, sai dai ana kallon tara yawan iyalai kamar na Mista Asilenu na neman wuce gona da iri.

Kofi Asilenu manomi ne kuma shekarun 'ya'yansa sun kama daga 50 zuwa goma sha daya, wasu daga cikinsu ba sa tare da shi don suna aiki a birni.

To ko me ya kai shi haihuwar 'ya'ya da dama haka?

"Bani da wani dan uwa ko kawu, shi ya sa na yanke shawarar na haifi 'ya'ya da dama saboda in samu wadanda za su yi mini jana'iza a mutunce idan na mutu. A garinmu mutumin da ya haifi da daya ana ganin girmansa, shi ya sa na haifi 'ya'ya da dama," in ji shi.

To ganin girman iyalinsa ko yaya yake iya ciyar da su? Ya bayyana cewa harkar cude ni in cude ka ake.

"A da ni mai kudi ne don haka na iya daukar nauyin iyalina."

Sai dai daukar nauyin 'ya'yan da ya haifa ya sa a yanzu babu kudin. Sai dai 'ya'yan nasa ne kuma ke taimaka masa.

Ya ce, "A yanzu wasu daga cikin 'ya'yana suna aiki kuma su suke taimaka mini wajen kulawa da iyalina sosai."

Mista Asilenu na da mata 12, kuma matarsa ta fari Nayome Asilenu ta ce duka matansa sun amince da wannan zama.

"Bayan mun yi aure sai mijina ya yanke shawarar kara aure sai ya zamo bani da wani zabi tunda dai yana kula da mu yana biyan kudin makarantar yara, suna cikin koshin lafiya saboda haka babu wani abin daga hankali."

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Obed Kwadwo dan sanda ne mai shekaru 40 a duniya kuma yana daga cikin 'ya'yan Kofi, ya yi karin haske kan yadda mahaifinsa ya dauki nauyin karatunsa.

A cewarsa, "A wancan lokacin mahaifina mai kudi ne saboda haka ya dauki nauyin karatuna har zuwa matakin babbar sakandare. Sai kuma abubuwa suka fara tsayawa ya zo ba ya iya kulawa da ni, don haka sai na yanke shawarar yin wani abu sai na shiga aikin dan sanda. Can kuma bayan abubuwa sun tsaya masa cak ni da sauran 'yan uwa ne sai muka ci gaba da taimaka masa."

Kofi Asilenu mutum ne da har yanzu yake da karfi kuma ya ce yana da muradin kara haihuwar 'ya'ya. Shekara uku da ta wuce a bisa rashin sani ya nemi 'yarsa da aure. Amma daga bisani ya nemi gafararta, tare da ya yi mata bayanin cewa yana da matsalar gani shi yasa bai gane ta ba.

A shekarun baya dai mutanen Ghana na son haihuwa da yawa saboda ana daukar hakan da cewa arziki ne. Kuma a wancan lokaci da Kofi Asilenu bai fita zakka ba.

Amma a yanzu abubuwa sun sauya. Ana kara jaddada muhimmancin amfani da hanyoyin tsara iyali a fadin kasar Ghana, don haka Kofi Asilenu ya fita zakka.

Labarai masu alaka