An kalli bidiyo mafi farin jini a YouTube sau sama da biliyan biyu

Hoton mawaki Psy daga wakarsa ta Gangnam Style Hakkin mallakar hoto Schoolboy/Universal Republic Records
Image caption Bidiyon wakar Gangnam Style shi ne mafi farin jini a YouTube har na tsawon shekara biyar

Bidiyon wakar Gangnam Style ya rasa kambunsa na bidiyon da a ka fi kallo a YouTube.

Wakar mai matukar farin jini ta dan asalin Koriya ta Kudu ita ce a ka fi kallo a shekara biyar da suka gabata.

Bidiyon ya yi farin jinin da har ya wuce ma'aunin YouTube da masu kallo miliyan 2,147,483,647, abin da ya tilastawa kamfanin su sake wallafa manhajar YouTube din saboda ba su yi tunanin wani bidiyo zai iya samun masu kallo biliyan biyu ba.

Amma wani bidiyon wata wakar ya kwace kambun daga hannun Gangnam Style - wakar Wiz Khalifa da Charlie Puth mai suna See You Again.

An kalli wannan bidiyon mai jan hankali sau biliyan 2,895,373,709; inda ya doke bidiyon na Psy mai alkaluman masu kallo na 2,894,426,475.

Idan kana son kallon bidion wakar See You Again na tsawon yawan da masu kallo suka ka yi wa wakar a YouTube, za ka dauki shekara 21,759 kafin ka gama kallonsa.

Hakkin mallakar hoto Atlantic Records
Image caption Mawaki Charlie Puth ne ya rubuta wakar See You Again, kuma Wiz Khalifa ya saka wasu baituka.

An rubuta wakar ne domin fim din Furious 7, kuma domin a karrama marigayi dan fim, Paul Walker wanda ya mutu a wani hatsarin mota kafin a kammala hada fim din.

Wakar ta See You Again ce a ka fi nema a wajen jana'iza a kasar Burtaniya saboda irin kalaman jan hankalin da ke cikinta.

Ita ce wakar da tafi kowace ciniki a shekarar 2015, kuma ta sami shiga jerin fitattun wakoki a bikin Grammys da na Oscars.

Hakkin mallakar hoto Universal Studios
Image caption Wakar ta karrama Paul Walker ne wanda ya mutu a sanadin hatsarin mota a lokacin da a ke hada fim din Furious 7

Bidiyon ya sami masu kallo biliyan daya a cikin wata shida, inda ya kai biliyan biyu a watan Satumbar da ya gabata.

Amma da alama bidiyon ba zai dade a kan karagar da ya ke kai ba na wani lokaci mai tsawo nan gaba.

Bidiyon mawaki Luis Fonsi na Despacito ya sami masu kallo biliyan 2.5 a cikin wata shida kacal.

Wakar da a ka rera ta a harshen Spaniyanci da Ingilishi ta zame ta daya a cikin dukkan wakoki a kasar Burtaniya cikin makonni takwas da suka gabata - amma da alama saka wasu baituka daga matashin mawaki Justin Bieber ya taimaka sosai.

A halin yanzu, fitattun bidiyo 47 cikin 50 da ke YouTube na wake-wake ne, abin da ya tabbatar da muhimmancin YouTube ga kamfanonin waka.

Hakkin mallakar hoto Universal Music
Image caption Despacito ce waka mafi farin jini a bana
Bidiyo mafi farin jini a YouTube
Mawaki Waka Yawan masu kallo (a lokacin hada wannan rahoton)
1) Wiz Khalifa See You Again (ft Charlie Puth) 2,895,373,709
2) Psy Gangnam Style 2,894,426,475
3) Justin Bieber Sorry 2,635,572,161
4) Mark Ronson Uptown Funk (ft Bruno Mars) 2,550,545,717
5) Luis Fonsi Despacito (ft Daddy Yankee) 2,482,502,747
6) Taylor Swift Shake It Off 2,248,761,095
7) Enrique Iglesias Bailando 2,232,756,228
8) Maroon 5 Sugar 2,150,365,635
9) Katy Perry Roar 2,129,400,973
10) Taylor Swift Blank Space 2,101,607,657

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba