Mata ne matsalar nahiyar Afirka - Macron

Emmanuel Macron Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu amfani da shafukan zumunta sun caccaki Mr Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya soki matan nahiyar Afirka saboda yawan haihuwar da suke yi.

Mr Macron ya bayyana haka ne ga manema labarai a wurin babban taron G20 a birnin Hamburg na kasar Jamus.

Ya ce Afirka na fuskantar matsaloli ne domin rashin "ci gaba", kuma yawan haihuwa shi ne dalilin da ya sa nahiyar ta kasa samun ci gaban tattalin arziki.

"Za a iya kashe biliyoyin euro, amma hakan ba zai gyara komai ba idan mata suka ci gaba da haihuwar 'ya'ya bakwai ko takwas", in ji Shugaba Macron.

Jaridar Vox ta soki kalaman shugaba Macron, inda ta ce sun nuna irin kallon raini da yake yi wa nahiyar Afirka.

Kazalika, masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi raddi ga shugaban na Faransa, inda suka nuna rashin jin dadinsu ga kalamansa.

Shugaba Macron ya kuma ce, "Kalubalen da ke gaban Afirka, daban ne, mai zurfi ne, matsalar wayewar kai ce. Matsalolin siyasa da na mulki suna cikin kalubalen da Afirka take fuskanta...

Saboda haka matsalolin safarar miyagun kwayoyi, da makamai, da mutane, da kayayyakin fasahar wani da "ra'ayin addini mai tsauri" da ta'addanci sune suke ta'azzara matsalolin Afirka. Amma duk da haka, akwai kasashen da suka sami ci gaba da nasarori, kuma wannan shi ne ya sa mutane suke kiran Afirka kasar arziki."

Labarai masu alaka