Nigeria: Majalisa ta yi dokar kulawa da wadanda aka harba da bindiga

Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty Images

Majalisar dattijan Najeriya ta zartar da wani kudirin doka wanda zai duba lamarin samar wa wadanda aka harba da bindiga kulawa a asibitoci.

Shugaban majalisar dattijai, Abubakar Bukola Saraki ya bayyana cewa ba kowanne mutum ne da aka haraba da bindiga mai laifi ba.

Saboda haka ya yaba da wannan kudurin dokar, wanda da zai rage yawan rasa rayukan wadanda aka harban.

Shugaban majalisar ya ce, "Wannan kudirin dokar da muka zartar zai tilasta wa dukkan asibitoci da ke Najeriya, ko na gwamnati ko masu zaman kansu, da su karbi duk mutumin da a ka harba da bindiga kuma asibitin ya ba shi kulawar da ya kamata cikin gaggawa, ba tare da la'akari da dalilin da ya janyo harbin ba."

"Ya kamata mu bar wa bangaren shari'a damarsu ta yanke hukunci, mu kuma bar wa ma'aikatan lafiya damarsu ta yin aikinsu", in ji Bukola Saraki.

Wani sashin kudirin dokar zai tilasta wa kowanne dan Najeriya, har da jami'an tsaro, da su taimakawa duk mutumin da ka harba, kana su tabbatar da an kai shi asibiti mafi kusa ba tare da bata lokaci ba.

Kuma laifi ne a karkashin kudirin dokar a ki ba wanda aka harba da bindiga kulawa a asibiti nan take ko da kuwa bai biya kudin ka'ida a asibitin ba.

Wannan kudurin dokar ya sosa wa jama'a da dama inda yake musu kaikayi, saboda a Najeriya mutane da dama kan fuskanci matsaloli saboda yadda jami'an tsaro ke kallonsu a matsayin wadanda suka aikata manyan laifuka da zaran an gan su da harbin bindiga.

Batun haka yake a asibitoci, inda likitoci da masu aikin kiwon lafiya ke kin karbar irin wadannan mutanen, saboda ba su tabbatar da dalilin da aka harbe su ba.

Labarai masu alaka