Me kuke son sani kan janyewar Etisalat daga Najeriya?

Hankalin masu amfani da Etisalat ya tashi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hankalin masu amfani da Etisalat ya tashi

Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya ta yi kira ga masu amfani da layin wayar salula na Etisalat da su kwantar da hankalinsu bayan kamfanin, wanda ke da hedkwata a Hadadiyar Daular Larabwa, ya tsame hannunsa daga reshensa da ke Najeriyar.

Kamfanin Etisalat Nigeria ya shiga cikin rudani ne bayan da ya kasa biyan basukan da wasu bankuna ke bin sa.

Me kuke son sani kan janyewar Etisalat din daga Najeriya?

Mun daina karbar tambayoyi ta wannan shafin. Mun gode.

Labarai masu alaka