Yemi Osinbajo ya yi 'kyakkyawar' ganawa da Buhari

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ziyarar da Osinbajo ya kai wa Buhari

Mukaddashin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a birnin London wanda ya kwashe fiye da wata biyu yana jinya a can.

Wata sanarwa da kakakin farfesa Osinbajo, Laolu Akande ya wallafa a shafinsa na Twitter, a daren Talata, ta ce "Nan ba da jimawa ba za mu sanar da jama'a yadda ganawa tsakanin shugabannin biyu ta kaya."

Sai dai ya kara da cewa, "shugabannin biyu sun yi kyakkyawar ganawa," inda rahotanni suka ce sun shafe sa'a guda tare.

Tuni dai Mr Osinbajo ya koma gida Najeriya inda zai jagoranci taron ministoci. Kuma ana sa ran zai yi karin haske kan ganawarsa da shugaban.

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa Shugaba Buhari ne ya bukaci mukaddashin shugaban kasar ya je wurinsa domin su tattauna kan wasu batutuwa.

Wannan dai shi ne karo na farko da mutanen biyu za su gana tun da shugaban na Najeriya ya fice daga kasar.


Me 'yan Najeriya ke sa ran ji daga Osinbajo?

Masu sharhi a Najeriya na ganin babban labarin da 'yan kasar ke jira su ji daga farfesa Yemi Osinbajo shi ne yanayin lafiyar shugaban kasancewar tunda ya bar kasar fiye da watanni biyu babu labarin hakikanin yanayin da Buhari yake ciki.

Sai dai kuma masu sharhin irin su Ja'afar Ja'afar na tsammanin mukaddashin shugaban zai bayar da bahasi kan batutuwa guda uku da "watakila Osinbajon yake bukatar tuntubar Buhari kafin ya zartar duk kuwa da cewa Buharin ya bai wa mukaddashin nasa wuka da nama."

Abubuwan da Ja'afar Ja'afar ya lissafa su ne:

 • Bahasi kan rahoton kwamitin da Farfesa Osinbajo ya jagoranta kan zargin badakalar cin hancin da ake yi wa sakataren gwamnatin kasar da aka dakatar, Babachir Lawal da shugaban hukumar leken asiri ta kasar, Ayo Oke.
 • Da kuma batun ministoci guda biyu da majalisar dattawan kasar ta wanke ranar uku ga watan Mayu amma mukaddashin shugaban bai rantsar da su ba.
 • Rashin fahimtar juna tsakanin bangaren majalisar dokoki da na zartarwa kan shugaban hukumar yaki da rashawa da cin hanci, Ibrahim Magu. Majalisar dokoki dai ta ki amince wa da Ibrahim Magu amma bangaren zartarwa ya kekashe kasa.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yemi Osinbajo

Ja'afar Ja'afar ya ce "A kasashen Afirka, mataimakin shugaban da aka ba shi rikon kwarya bai cika yin gaban kansa ba wajen zartar da hukunce-hukunce duk kuwa da cewa tsarin mulki ya ba shi dama."

Ya kara da cewa "wani lokacin mukaddashin shugaban kasa ya kan bar hakkinsa a wasu lokutan domin girmama shugaban nasa da kuma son zama lafiya da mutanen da suka kankane shugaban."

A watan Maris ne din shekarar 2017 ne dai shugaba Buhari ya dawo daga hutun jinya na mako bakwai a Birtaniya, sannan ya koma a watan Mayu.

A lokacin da ya dawo daga London, Shugaba Buhari ya ce bai taba yin rashin lafiya irin wacce ya kwanta ba.

Ya ce an kara masa jini ko da yake bai fadi cutar da ke damunsa ba.


Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

Image caption A watan Maris Shugaba Buhari ya yi jinyar mako bakwai a London
 • 19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"
 • 5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
 • 10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
 • 26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
 • 28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba
 • 3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
 • 5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu
 • 7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya