Majalisar dokokin Amurka ta gayyaci dan Donald Trump

Trump
Image caption Shugaba Trump da dansa Donald Trump Junior.

'Yan majalisar dokokin Amurka sun nemi dan gidan Shugaban kasar, Donald Trump Junior da ya bayyana a gabansu kan batun mallakar bayanan batanci ga abokiyar takarar mahaifinsa, Hillary Clinton.

Donald Trump Junior dai ya ce bai yi wa mahaifinsa magana ba kan haduwa da wata lauya 'yar kasar Russia wadda ta nemi ta tallafa wa yakin gangamin zaben Trump, da bayanan batanci ga Hillary Clinton, a bara.

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Chuck Schumer ya nemi dan gidan shugaban tare da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar da su bayyana a gabansu domin in gamsasshen bayani.

A wata hira da gidan talbijin na Fox News , Donald Trump Junior ya bayyana haduwa da lauyar da wani abun da bai kai ya kawo ba.

Ya ce "idan na waiwayi al'amarin ina ganin ya kamata na yi wani abu daban da hakan. Kuma wannan dai wani shaci fadin jaridun Russia ne kawai amma ba abun da haduwar tamu ta tattauna a kai ba kenan."

Sai dai kuma da farko Trump Junior ya saki wasu jerin sakonni imail da ke nuna yadda ya yi maraba da bukatar haduwa da lauyar 'yan kasar ta Russia.

Manyan 'yan majalisar dokokin Amurkar dai sun bayyana bayanan da ke cikin sakonni imail din da Trump Junior ya saki da abun takaici.

Yanzu haka dai ana ganin kokarin da gwamnatin mista Trump ta yi na nesanta kanta da Russia yana neman ya zama yaudara.