Kunsan hanyoyin rage iska mai guba da ke gurbata mahali?

iska kan teku Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption iska a cikin ruwa

Wasu kwarrarun masana a jami'ar Lund a Switzerland sun gudanar da wani bincike, kan hanyoyi mafi tasiri ga jama'a wajen rage yawan samar da iska mai guba wato Carbon dioxide .

To sai dai tuni jama'a suka fara korafin cewa binciken ya fuskanci munmunar alkibbila.

Masu binciken kimiyar sun sanar da cewa amfani da abinci wanda ya samu tushe daga tsirrai da kaucewa yin balaguro ta jirgin sama da yin rayuwa ba mota da kuma kasancewa da yara kalilan, duk wadanan abubuwa na rage yawan iska mai gurbata muhali na Carbon dioxide .

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption iska mai gurbata mahali

To sai dai wasu da dama da alama ba su amanna da wannan bincike ba kamar yadda bayanai suka nuna daga kalaman da jama'ar suka yi a kansa .

To sai dai matakan da gwamnatocin Amurika da Canada da Australia da kuma na kasashen turai suka dauka , sun danganta ne ga sauyin gudanar da yanayin tafiyar da rayuwa da ke da alaka ko kuma kusanci da sake yin anfani da abubuwan da aka yin anfani da su a baya ta hanyar sake sarrafasu, domin a kara yin wani amfani da su na daban.

Binciken ya gano cewa iyalai a Amurika sun kwammace su samu da daya ko kuma su zauna babu dan, da su kasance da irin tasirin da iska mai guba zai yi a kansu kamar na yara masu shekaru 10, guda dari shida da 84 ,da za su yi a dukan tsawon rayuwarsu.

Labarai masu alaka