Nigeria: Kun san abin da Osinbajo ya gayawa Buhari?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ziyarar da Osinbajo ya kai wa Buhari

Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya yi karin haske kan tattaunawar da ya yi da Shugaba Muhamamdu Buhari a ranar Talata a London.

Shugabannin biyu sun shafe sama da sa'a guda suna tattaunawa, wacce ita ce ganawar su ta farko tun bayan tafiyar shugaban jinya wata biyu da ya gabata.

Kawo yanzu dai ba a bayyana cutar da Shugaba Buhari ke fama da ita ba.

Hakkin mallakar hoto Nigerian Government
Image caption Osinbajo a lokacin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida

Ga abin da Osinbajo ya ce sun tattauna da mai gidan nasa:

"Da farko kamar yadda kuka sani, na je ne in duba lafiyarsa domin in san yadda yake ji.

Kuma daman ina magana da shi ta waya, sai na ga ya dace in je in gan shi kuma in ga irin halin da yake ciki tare da ba shi labarin abubuwan da ke aukuwa a gida.

Saboda haka, mun tattauna da kyau kan abubuwa da dama kuma yana cike da annashuwa. Yana samun sauki sosai."

'Yan jarida sun tambaye shi:

Yaya jikin shugaban kasar?

E, kamar yadda na ce yana cikin annashuwa, yana samun sauki sosai. Kuma mun yi tattaunawa ta tsawon lokaci. Mun shafe fiye da sa'a daya muna tattaunawa, kuma yana nan kamar yadda aka san shi da raharsa. Yana samun sauki sosai.

Yaushe zai dawo?

Ina ganin a nan gaba kadan. Nan ba da jimawa ba. Ina ganin ya kamata mu tsammanci dawowarsa. Kamar yadda na fada yana samun sauki sosai.

Kun tattauna kan batun sakataren gwamnatin tarayyar da shugaban hukumar leken asiri?

Batutuwa da dama ne. Ba zan iya bayayya batutuwan da muka tattauna ba dalla-dalla.

Kun tattauna batun rantsar da ministoci biyu?

A'a. Ba mu tattauna batun rantsar da su ba.

Shin muna tsammanin shugaban kasa zai dawo nan da kwana 90?

A'a. Wa'adi ba abu ne mai kyau ba, amman kamar yadda na fada yana samun sauki sosai. Muna tsammanin zuwansa nan ba da jimawa ba, fiye da yadda ku ke tsammani.


Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

Image caption A watan Maris Shugaba Buhari ya yi jinyar mako bakwai a London
  • 19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"
  • 5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
  • 10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
  • 26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
  • 28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba
  • 3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
  • 5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu
  • 7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya

Labarai masu alaka