Nigeria: Kotu ta ce Ahmed Makarfi ne halattaccen shugaban PDP

PDP
Image caption Rikicin ya raba kawunan 'ya'yan jam'iyyar a sassan kasar daban-daban

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da Sanata Ahmed Makarfi a matsayin halattaccen shugaban jam'iyyar adawa ta PDP.

Wannan hukunci na nufin bangaren Sanata Ali Modu Sheriff ba za su iya daukaka kara ba.

Shekara biyu kenan ana rikicin shugabanci a jam'iyyar wacce ta shafe shekara 16 tana mulkin kasar.

Lamarin da raba kawunan 'ya'yan jam'iyyar a sassan kasar daban-daban.

Rahotanni sun ce jami'an bangaren Ahmed Makarfi da suka halarci zaman kotun, sun nuna farin cikinsu ga hukuncin.

Sai dai kawo yanzu babu wani martani da ya fito daga bangaren Ali Modu Sheriff da suka sha kaye.

Tuni wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar suka yi maraba da hukuncin.

Tsohon kakakin jam'iyyar Cif Olisa Metuh ya bayyana cewa babu wanda ya yi nasara ko ya fadi sakamakon hukuncin, yana mai cewa dama ce ta a hadu tare domin inganta jam'iyyar.

A wata sanarwa da ya fitar, ya ce wajibi ne "mu sake bude kofa ga dukkan 'yan Najeriya da ke son ganin tsarin demokuradiyya ya tabbata".

Mun dauki kaddara

A lokacin da yake mayar da martani, Ahmed Gulak, wanda yana cikin masu goyon bayan bangaren Ali Modu Sheriff ya ce sun gamsu da hukuncin da kotun koli ta yanke kuma "mun dauki kaddara".

Ya ce sun karbi hukuncin kotun kolin ne domin kotun ce matakin karshe na shari'a a Najeriya.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
PDP da APC abu daya ne - Nuhu Ribadu

Shi ma mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ike Ekweremadu, ya ce "Hukuncin kotun kolin zai samar da wata dama ta wanzar da dauwamammen zaman lafiya da sasanta mambobin jam'iyyar ta PDP".

"Ina farin ciki da hukuncin kotun koli inda ta kawo karshen wannan rikicin da yaki-ci-yaki-cinyewa, wannan nasara ce ta jam'iyyarmu da demokuradiyya a kasarmu baki daya," in ji Sanata Ekweremadu.

Me ya raba PDP da APC?

An dade ana zargin jam'iyyun siyasar Najeriya da rashin akida, inda suke mayar da neman mulki babbar munufarsu.

A wata hira da BBC a kwanakin baya, tsohon shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC, Mallam Nuhu Ribadu, ya shaida wa BBC cewa babu wani cikakken banbanci tsakanin jam'iyyun PDP da APC.

Labarai masu alaka