Masoya Everton sun yi wa Rooney babbar tarba

Ana ta yi wa Rooney maraba
Image caption Masoya Rooney sun yi matukar farin cikin ganinsa a Tanzania

Kulob din Everton ya isa Dar es Salaam, babban birnin kasar Tanzania, a wani rangadi irinsa na farko da kungiyar ta taba yi a Afrika.

Randagin dai wani bangare ne na wasannin sa da zumunta domin share fagen kakar wasannin Firimiya na shekarar 2017 zuwa 2018.

Everton ta kammala kakar wasanni na bara tana mataki na bakwai a teburin Firimiya kuma ta washe baki daya 'yan wasan rukunin farko zuwa Tanzania.

Tawagar dai ta isa babban filin jiragen sama da ke Dar es Salaam da safiyar Laraba bayan sun taso daga birnin Liverpool na Birtaniya.

Cikin 'yan wasan sun hada da Wayne Rooney, wanda ya koma kulob din da ya fara taka wa leda tun yana matashi, daga Manchester United a karshen mako.

Ana sa ran dan wasan zai buga wa Everton tamaula ta farko a karawar da Everton za ta yi da kungiyar kwallon kafa ta Kenya Gor Mafia a filin wasa na kasa da ke Dar es Salaam, mai daukar mutane 60,000.

Masoyan kulob din da dama ne daga makwabtan kasashe suka isa Tanzania domin kallon wasan.

Image caption Masoyan Yannick Bolasie sun je Tanzania daga Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo domin yin tozali da gwarzon nasu

Wasu kuma sun taru a Otel din da tawagar ta sauka suna rera waka da sunan "Rooney, Rooney" a yayin da dan wasan ya fito daga motar da ta dauko su.

Haka kuma akwai masoyan Yannick Bolasie, wadanda suka zo daga Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo domin yin tozali da gwarzon nasu. Sun yi ta kida da waka irin na gargajiya, yayin da shi kuma Bolasie ya taka rawa.

Karawar da za a yi a ranar Alhamis wani bangare ne na daukar nauyin sabuwar rigar Everton wanda kamfanin Sport Pesa ya yi.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kabilar Masaai sun yi ta kida da waka na gargajiya don yi musu maraba da zuwa Tanzania

A yayin rangadin kuma 'yan wasan kulob din za su bayar da dan horo tare da buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta zabiya domin wayar da kan mutane su daina kai musu hari.

Ana kashe zabiya a Tanzania saboda tsafi da wasu sassan jikinsu.

Labarai masu alaka