'Muna sa ran dawowar Buhari nan ba da jimawa ba'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ziyarar da Osinbajo ya kai wa Buhari

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce nan ba da jimawa ba shugaba Buhari zai dawo daga London inda ya je jinyar rashin lafiya.

Farfesa Osinbajo ya bayyana hakan ne ga manema labarai a fadar gwamnatin kasar a ranar Laraba, gabannin taron majalisar ministocin kasar.

Mukaddashin shugaban kasar ya kuma ce shugaba Buharin yana samun sauki sosai-sosai, don haka 'muna sa ran dawowarsa nan kusa.'

A ranar Laraba ne Farfesa Osinbajo ya tafi London domin duba Shugaba Buhari wanda ya kwashe fiye da wata biyu yana jinya a can.

Kakakin farfesa Osinbajo, Laolu Akande ya ce "shugabannin biyu sun yi kyakkyawar ganawa," inda rahotanni suka ce sun shafe sa'a guda tare.

Image caption Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osibanjo ya ce shugaba Buhari na murmurewa

Sai dai kuma Farfesa Osinbajo bai yi wani karin bayani kan yadda tattaunawar ta su ta kasance da shugaba Buhari ba.

Ta iya yiwuwa zai yi karin bayanin ne a yayin zaman majalisar da zai jagoranta din ko kuma bayan an kammala.

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

  • 19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"
  • 5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
  • 10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
  • 26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
  • 28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba
  • 3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
  • 5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu
  • 7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya

Labarai masu alaka