Yaushe rabon Buhari da Nigeria?

  • Nasidi Adamu Yahya
  • BBC Hausa
Bayanan bidiyo,

Ku kalli bidiyon gidan da Buhari yake jinya a London

A ranar Alhamis din nan ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya cika kwana 74 da ficewa daga kasar zuwa birnin London, domin jinyar cutar da ba a bayyana ba.

Shugaban ya tafi Burtaniya ne ranar bakwai ga watan Mayu, jim kadan bayan ya gana da 'yan matan makarantar Chibok 81 wadanda aka sako kwana daya kafin tafiyar tasa.

Tun da shugaban kasar ya fice daga Najeriya dai 'yan kasar ke dokin ganinsa, sai dai fadar shugaban kasar ta ce ba ta san ranar da zai koma gida ba.

A ranar 11 ga watan nan ne Mukaddashin Shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da Shugaba Buhari a birnin London.

Bayan komawarsa Najeriya, Mr Osinbajo ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa nan ba da dadewa ba shugaban zai koma gida.

Ga cikakkiyar hirarsa da manema labarai:

"Da farko kamar yadda kuka sani, na je ne in duba lafiyarsa domin in san yadda yake ji.

Kuma daman ina magana da shi ta waya, sai na ga ya dace in je in gan shi kuma in ga irin halin da yake ciki tare da ba shi labarin abubuwan da ke aukuwa a gida.

Saboda haka, mun tattauna da kyau kan abubuwa da dama kuma yana cike da annashuwa. Yana samun sauki sosai."

Yaya jikin shugaban kasar?

E, kamar yadda na ce yana cikin annashuwa, yana samun sauki sosai. Kuma mun yi tattaunawa ta tsawon lokaci. Mun shafe fiye da sa'a daya muna tattaunawa, kuma yana nan kamar yadda aka san shi da raharsa. Yana samun sauki sosai.

Bayanan hoto,

A farkon shekarar nan ma Shugaba Buhari ya yi jinyar mako bakwai a London

Yaushe zai dawo?

Ina ganin a nan gaba kadan. Nan ba da jimawa ba. Ina ganin ya kamata mu tsammanci dawowarsa. Kamar yadda na fada yana samun sauki sosai.

Kun tattauna kan batun sakataren gwamnatin tarayyar da shugaban hukumar leken asiri?

Batutuwa da dama ne. Ba zan iya bayayya batutuwan da muka tattauna ba dalla-dalla.

Kun tattauna batun rantsar da ministoci biyu?

A'a. Ba mu tattauna batun rantsar da su ba.

Shin muna tsammanin shugaban kasa zai dawo nan da kwana 90?

A'a. Wa'adi ba abu ne mai kyau ba, amman kamar yadda na fada yana samun sauki sosai. Muna tsammanin zuwansa nan ba da jimawa ba, fiye da yadda ku ke tsammani.

Baya ga duba lafiyar shugaban kasar, Mista Osinbajo ya ce, "Na ba shi [Buhari] labarin abubuwan da ke aukuwa a gida. Mun tattauna da kyau kan abubuwa da dama kuma yana cike da annashuwa."

Kulle-kullen siyasa

Wasu na ganin ci gaba da zaman da Shugaba Buhari ke yi a London shi ya sa wasu 'yan siyasa ke kulle-kullen ganin sun maye gurbinsa da wani fitaccen dan siyasa.

A kwanakin baya ne dai majalisar dattawan kasar ta tayar da kura bayan wasu 'yan majalisar sun nemi a rantsar da shugabansu Bukola Saraki a matsayin mukaddashin shugaban kasa.

A cewarsu, tafiyar Farfesa Osinbajo zuwa Habasha domin halartar taron kungiyar kasashen Afirka kana kuma Shugaba Buhari yana kwance a London, ta sa an samu gurbi a shugabancin kasar.

Sai dai Mista Saraki ya yi watsi da bukatar sanatocin.

Asalin hoton, Nigerian Government

Bayanan hoto,

Yemi Osinbajo ne ke gudanar da al'amura a madadin Shugaba Buhari ciki har da halartar taron Kungiyar Tarayyar Afirka

Wani batu kuma da ya nuna cewa akwai walakin goro a miya shi ne yadda mai dakin shugaban kasar Aisha Buhari ta wallafa wani sako a shafinta na Facebook inda take gugar zana kan al'amuran da suke faruwa a gwamnatin mijinta, tun bayan tafiyarsa jinya.

Misis Buhari ta ce mijinta na samun sauki kuma zai koma kasar domin ya yi maganin azzalumai.

A cewarta, "Allah ya amsa addu'ar kananan dabbobi [wato talakawa], nan ba da dadewa ba za a fatattaki kuraye da dila daga dawa. Mun matukar yarda da addu'a da goyon bayan kananan dabbobi [talakawa]. Allah ya ja zamanin talakawa, Allah ya ja zamanin Najeriya."

Masana harkokin siyasa na ganin habaicin nata ba ya rasa nasaba da irin kulle-kullen siyasar da wasu da ke kusa da shugaban kasar da ake gani sun hana ruwa gudu ke yi.

Da ma dai ba wannan ne karon farko da matar shugaban kasar ke fitowa fili tana sukar makusantan shugaban kasar ba, wadanda ta ce cima-zaune ne da suka hana sakawa 'yan jam'iyyar APC kan goyon bayan da suka bai wa Shugaba Buhari lokacin har ya kai ga lashe zaben 2015.

Babu wanda ya san cutar da ke damun shugaban na Najeriya, mai shekara 74, kuma ba a ganshi a bainar jama'a ba tun bayan tafiyar sa London.

Mukarrabansa sun sha nanata cewa Shugaba Buhari da likitocinsa ne kawai za su iya fada wa duniya abin da ke damunsa.

Sai dai a lokacin da ya koma kasar daga jinya a watan Fabrairu, ya ce an kara masa jini kuma bai taba fama da rashin lafiya irin wacce ya kwanta a lokacin ba.

Asalin hoton, Aisha Twitter

Bayanan hoto,

Matar Shugaba Buhari ta sha tayar da kura kan batutuwan da suka shafi gwamnati

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"

5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya

10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba

26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"

28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba

3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku

5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu

7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya

25 ga watan Yuni - Ya aikowa 'yan Najeriya sakon murya

11 ga watan Yuli - Osinbajo ya gana da shi a London