Kotu ta yanke wa tsohon shugaban Brazil hukuncin daurin shekara tara da rabi

Lula ya lashe zabe a shekarar 2003 da 2006 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Lula ya lashe zabe a shekarar 2003 da 2006

Wasu takardun kotu sun nuna cewa an yanke wa tsohon shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva hukuncin daurin shekara tara da rabi saboda samun sa da laifin cin hanci.

An fahimci cewa Mr da Silva zai ci gaba da harkokinsa idan ya daukaka kara.

Lula ya yi watsi da zarge-zargen da aka yi masa na karbar hancin wani gida domin ya yi wasu alfarma a kamfanin man fetur na kasar Petrobras.

Ya ce an tuhume shi da laifukan ne domin a cimma wasu bukatu na siyasa.

Wannan hukunci shi ne na farko a cikin tuhuma biyar da ake zargin da laifi.

Lula ya kwashe shekara takwas a matsayin shugaban kasar Brazil inda ya sauka a 2011 kuma ya ce mai yiwuwa ya sake tsayawa takara a shekara mai zuwa karkashin jam'iyyar Workers' Party.

Ranar Laraba, wani alkali ya same shi da laifin karbar hanci daga wurin wani kamfanin injiniya OAS domin ya ba shi kwagila a kamfanin man kasar.

Labarai masu alaka

Karin bayani