‘Ku kalli bidiyon gidan da Buhari yake jinya a London’
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ku kalli bidiyon gidan da Buhari yake jinya a London

BBC Hausa ta ziyarci gidan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke jinya a birnin London.

Shugaban na Najeriya, wanda ya kwashe sama da wata biyu a Birtaniya, yana fama da cutar da ba a bayyanawa 'yan kasar ba.

A ranar Laraba ne mukaddashin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da shugaba Buhari a London inda ya ce nan ba da dadewa shugaban zai koma Najeriya.

  • 5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
  • 10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
  • 26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
  • 28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba
  • 3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
  • 5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu
  • 7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya

Labarai masu alaka