Kifi ya kashe wani mutum bayan ya cece shi

Tyler Howlett, left, pictured with his father Joseph Howlett, right Hakkin mallakar hoto Facebook / Tyler Howlett
Image caption Mista Howlett ne daga dama jim kada kafin kifin ya kashe shi

Wani katon kifi giwar teku ya kashe wani mutum dan kasar Canada bayan da ya ceto kifin daga hallaka sakamakon nannade shi da fatsa ta yi.

Joe Howlett ya yi nasarar ceto kifin, amma jim kadan sai kifin ya buge mutumin a daidai lokacin da yake komawa cikin ruwa.

Mutumin masunci ne kuma shi ne ya kirkiri wata kungiyar ceto a Tsibirin Campobello a New Brunswick.

Abokansa sun shaida wa kafofin watsa labaran Canada cewa ya ceci gomman giwar teku a shekara 15 da ta gabata.

Wani abokin Mr Howlett, Mackie Green, wanda da taimakonsa aka kirkiro tawagar masu ceton, ya ce, "Sun cire kifin daga jikin fatsar gaba daya, kawai sai wani abu da ba a zata ba ya faru, inda kifin ya yi wata girgiza ya buge shi.

Kifin dai irin wanda aka fi samu a Arewacin Tekun Atlantika ne, wani dabba ne mai hatsari wanda girmansa ke kai wa tsawon mita 15, nauyinsa kuma ya kai tan 70.

Kifin na da hatsari, kuma irinsa da suka rage ba su fi 500 ba, a cewar Hukumar Kula da Teku da Sararin Samaniya ta Amurka.

A watan da ya gabata ne aka samu gawar giwar teku bakwai a gabar tekun Canada na St Laurence, wanda hakan ya zama wani koma-baya wajen karuwar yawan giwar tekun.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kifin giwar teku da ya kashe Mista Hewlett kenan

A lokacin da wannan al'amari ya rutsa da Mista Howlett yana cikin jirgin ruwa ne na gwamnati mai bayar da agaji.

Hukumar Kula da Teku da Kifaye ta ce ko a ranar 5 ga watan Yuli ma ya ceci wani giwar teku.

"Mutane irin su Mista Howlett suna da jarumta da kokarin ganin sun bayar da taimakon su ga dabbobin da ke rayuwa a cikin ruwa," in ji Hukumar.

Mista Howlett ya yi rayuwarsa ne a Tsibirin Campobello, wani karamin yanki da ke iyakar Amurka, kuma a can ne mazauna yankin ke ta yin alhini tare da karrama shi.

Magajin garin Tsibirin, Stephen Smart, ya ce, "Mutum 850 ne kawai ke rayuwa a tsibirin nan, kuma Joe mutumin kirki ne mai barkwanci.

"Kowa ya san Joe Howlett kuma kowa yana girmama shi.... mutuwarsa ta zama tamkar bugun dalma a gare mu.

Labarai masu alaka

Karin bayani