Ambaliya: Jihohi 16 za su samu tallafi daga gwamnatin Najeriya

Ambaliyar ruwa a birnin Legas Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ambaliyar ruwa a birnin Legas

Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya bayar da umarnin da a fitar da naira biliyan 1.6 domin bayar da tallafin gaggawa ga wadanda bala'in ambaliya ya shafa a jihohi 16.

Jihohi sha shidan da ambaliyar ruwa ta yi wa ta'adi sun hada da Ekiti, da Osun, da Akwa-Ibom da Kebbi da Naija da kwara da Ebonyi da Enugu. Sai kuma Abia da Oyo da Legas da Filato da Sakkwato da Edo da kuma Bayelsa.

Mista Osinbajo ya sanar da hakan ne a lokacin da yake shugabantar taron majalisar zartarwar kasar, sa'o'i kadan bayan dawowarsa daga Landan, inda ya gana da Shugaba Buhari.

Za a fitar da kudin ne daga asusun da gwamnatin tarayya ke ajiye kudaden kula da muhalli wanda ke babban bankin kasa.

Haka kuma mukaddashin shugaban kasa ya amince cewa kwamitin shugaban kasa mai kula da bayar da agaji ga wadanda ambaliya ta shafa PCFRR shi ma ya bayar da karin gudunmawa.

Labarai masu alaka