Nigeria: Ta yaya janyewar Etisalat zai shafe ku?

Etisalat Nigeria Hakkin mallakar hoto .
Image caption Etisalat Nigeria ya samu mutum miliyan 21 da suke amfani da layinsa

Tun da uwar kamfanin Etisalat ta yi shelar ficewa daga Najeriya, 'yan kasar da ke hulda da kamfanin suka fara fargabar yadda wannan matakin zai shafe su.

Daya daga cikin batutuwan da ke damun mutane kimanin miliyan 21 shi ne halin da layukansu na Etisalat za su shiga bayan wa'adin mako uku da uwar kamfanin ta bayar na a daina amfani da sunan Etisalat a Najeriya.

Sai dai kuma lokacin da aka sayar da kamfanin sadarwa mai zaman kansa na farko a Najeriya, Econet, sunan ne kawai ya sauya, kuma mutane sun ci gaba da amfani da layukansu ba tare da wata matsala ba.

Kamfanin ya zama Vodaphone kafin ya zama Vmobile, sannan ya zama Celtel.

Daga baya ya zama Zain kafin ya zama Airtel da ake kiransa yanzu.

Har ila yau, akwai masu amfani da lambar wayar kamfanin tun lokacin da ya fara aiki da sunan Econet.

A wata sanarwar da hukumar da ke sa ido kan kamfanonin sadarwa a Najeriya ta fitar tun lokacin da gamayyar bankunan da ke bin kamfanin Etisalat Nigeria bashi suka yi barazanar kwace Etisalat na Najeriya, hukumar ta tabbatar wa masu amfani da layukan cewa za ta dauki daukkan matakin da ya dace wajen ganin cewa masu amfani da layukan sun ci gaba da amfani da shi duk da matsalar bashin.

Tarihin Bashin

Mutane na son sanin asalin tarihin bashin da ya janyo wa kamfanin matsala.

A shekarar 2013, kamfanin Etisalat Nigeria ya karbi bashin dala biliyan 1.2 daga bankunan kasar 13 domin ya samu ya ci gaba da biyan kudin ruwa kan bashin dala miliyan 650 da ake binsa da kuma sabunta na'urorinsa domin inganta aikinsa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kashi 14 chikin 100 na masu amfani da wayar salula a Najeriya suna amfani da layin Etisalat ne

Amma kamfanin ya kasa ci gaba da biyan kason da yake mayarwa daga cikin bashin a wannan shekarar saboda karayar tattalin arzikin da Najeriya ta shiga da kuma tsadar dala a kasuwar bankunan kasar.

Wannan ne ya sa bankunan kasar da ke bin kamfanin Etisalat Nigeria bashi suka ce ko kamfanin ya ci gaba da biyansu kafin sha 15 ga watan Yuni, ko kuma su kwace ragamarsa.

Jin haka, sai uwar kamfanin Etisalat da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi shelar janye hannun jarinta (kashi 70 cikin 100) daga kamfanin inda ta bar wa kamfanin Emerging Markets Telecommunication Services limited (EMTS) sauran kashi 30 din.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Babban bankin Najeriya ne ya hada kai da NCC wajen kai wa kamfanin Etisalat Nigeria dauki domin kare harkar kudin kasar

Domin a hana matsalar tattalin arzikin da kasar ka iya fadawa tare da salwantar ayyukan sama da mutum 4,000 idan bankunan 13 suka karbe iko da kamfanin Etisalat Nigeria, sai hukumar NCC mai sa ido kan harkar sadarwa da kuma babban bankin Najeriya, CBN, suka dauki matakin hana bankunan karbar iko da Etisalat Nigeria.

Matakin da bankunan da hukumar NCC suka dauka na samar da shirin sake fasalin kamfanin Etisalat Nigeria, ya sa jami'an gudanarwar kamfanin daga kamfanin EMTS karkashin jagorancin Hakeem Bello-Osagie suka yi murabus kuma aka nada wasu sabbin jami'an gudanarwar.

A cikin shirin sake fasalin kamfanin, wanda gamayyar bankunan da ke bin Etisalat Nigeria bashi ke samarwa tare da NCC da CBN, ana sa ran kamfanin Etisalat Nigeria zai zama mai dorewa ta hanyar cin riba da kuma iya biyan bashin da ake binsa.

Sai dai kuma bayan an fara shirin sake fasalin kamafanin ne uwar kamfanin ta ba da sanarwar cewa za ta janye sunanta daga Najeriya.

A hirar da ya yi da kamfanin dillancin labaran Reuters ranar Litinin, shugaban uwar kamafanin, Hatem Dowidar, ya ce nan da mako uku za a daina amfani da sunan kamfaninsu a Najeriya.

Duk da haka, kamfanin EMTS ya ce yana da yarjejeniya mai aiki da uwar kamfanin Etisalat na ci gaba da amfani da sunan kamfanin a Najeriya duk da sauye-sauyen da aka samu kwanan nan.

Shugaban kamfanin sadarwar, wanda shi ne na hudu a Najeriya bayan MTN da Globacon da kuma Airtel, Boye Olusanya, ya shaida wa Reuters cewa kamaninsa na ci gaba da tattaunawa da uwar kamfanin Etisalat domin ta bari a ci gaba da amfani da sunanta a Njaeriya.

Ya ce in har ba a cimma matsaya a tattaunawar ba, za a sake wa Etisalat Nigeria suna ne.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fiye da mutum 4,000 ne ke aiki a kamfanin Etisalat Nigeria

Duk da cewa kamfanin zai iya ci gaba da aiki da jarin da yake da shi a halin yanzu, Mista Olusanya ya ce mai-yiwuwa ne a sake karfafa jarin kamfanin ta hanyar sayar da hannayen jari.

Kamfanin Etisalat Nigeria ya fitar da wata sanarwar inda yake cewa janyewar uwar kamafanin daga Najeriya ba ya nufin kamfanin ya daina aiki ba ne.

Sanarwar da wani babban jami'i a kamfanin, Ibrahim Dikko, ya sanya wa hannu ta ce janyewar na nufin za a daina amafani ne da sunan Etisalat, inda nan ba da jimawa ba za a sa mai sabon suna.

Kalubalen da kamfanin da masu ruwa da tsaki a lamarin ke fuskanta shi ne iya kare aikin fiye da mutum 4,000 da suke aiki a kamfanin, baya ga kare layukan mutum miliyan 21 da ke amfani da layukan kamfanin a Najeriya.

Labarai masu alaka