An halatta auren jinsi guda a Malta

Joseph Muscat Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Firaiminista Joseph Muscat ya ce dokar abar yabawa ce

A kasar Malta, Majalisar Dokoki ta amince da dokar da ya yarje wa 'yan kasar yin auren jinsi guda wato mace ta auri mace namiji ya auri namiji.

Kusan dai za a iya cewa 'yan majalisar sun yi baki guda wajen amincewa da dokar.

Dokar dai za ta maye gurbin kalmar da aka fi amfani da ita ga masu aure ta miji da mata da kalmar abokan zama.

Malta wadda kasa ce da mabiya darikar katolika suke da rinjaye, ta kasance kasa ta 15 a jerin kasashen kungiyar Tarayyar Turai da suka amince da auren na jinsi guda.

Wannan dai na daya daga cikin alkawuran da Firai Minista Joseph Muscat ya yi lokacin yakin neman zabe.

Hakan a cewar Mista Joseph, na nuna irin yadda mulkin dimkoradiyyar ke kara tumbatsa a kasar.

Labarai masu alaka