Trump: shugaba Putin mutumina ne sosai

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shugaban Russia, Vladimir Putin mutuminsa ne kuma yana tuntubar sa sosai.

Kafar watsa labaran Christian Broadcasting Network ce dai ta yi hira da shi 'yan kwanaki bayan haduwarsa da mista Putin a taron kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki na duniya a Hamburg.

Sai dai kuma mista Trump ya kara da cewa yana da masaniyar cewa shugaban Russia zai fi so ace Hillary Clinton cea fadar White House, saboda zai so yin amfani da raunin da take da shi.

Yanzu haka dai ana ta gudanar da bincike iri-iri kan duba yiwuwar hannun Russia a cin zaben mista Trump.

Mista Trump dai ya sha musanta zargin kuma ita haka Russia ta nesanta kanta da shiga sharri ba shanu.

Dangane da ganawa da mista Putin, Trump ya ce "mutane sun ce bai kamata mu gana ba. tambayar a nan ita ce su wane ne wadannan mutanen. ina tunanin muna ganawa a kai a kai.

"Amurka da Russia kasashe ne masu karfin makamin nukiliya saboda haka ai babu hankali a maganar cewa bai kamata mu kulla a alaka ba."

Mista Trump ya kuma bayyana yarjejeniyar tsagaita wutar da kasashen biyu suka cimma a kudu maso yammacin kasar Syria da fa'idar da ke tattare da kulla alaka tsakanin kasashen.

Donald Trump Jr 'ba shi da laifi'

Mista Trump dai da farko ya wanke dansa Donald Juniro kan haduwarsa da lauyar nan 'yar kasar Russia a 2016 lokacin da yakin neman zaben Amurka ya yi zafi.

Dan na mista Trump ya gana da lauyar ne mai suna Natalia Veselnitskaya a Trump Tower da ke birnin New York a watan Yunin 2016.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cece-kuce kan haduwar Donald Trump Junior da Natalia Veselnitskaya

Trump Junior dai ya samu labarin cewa lauyar na dauke da bayanan da za su zubarwa Hillary Clinton kima.