Ghana: 'Yan wasan kulob din Asante Kotoko sun yi hadari

Motar 'yan wasan Asante Hakkin mallakar hoto Asantekotokos.com

Rahotanni daga kasar Ghana na cewa 'yan wasan fitacciyar kungiyar kwallon kafa kuma dadaddiya a kasar, Asante Kotoko, sun yi mummunan hadarin mota.

Tawagar 'yan wasan na kan hanyar dawowa ne daga birnin Kumasi, bayan kammala gasar premier league da aka yi tsakanin kulob din da Inter Allies FC na kasar.

Lamarin dai ya faru ne a garin Nkawkaw mai nisan tafiyar kilomita 150 daga babban birnin kasar Accra.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba, sun ce 'yan wasan sun ji mummunan rauni, ya yin da ake zaton mai kula da kayan 'yan wasa Mista Asare ne ya riga mu gidan gaskiya.

Ya yin da kociyan kungiyar kwallon kafar Coach Polack, da mataimakin sa Godwin Ablordey da kuma direban motar Bus din na cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Labarai masu alaka