'Yan majalisa sun bukaci a dawo da shugaban NHIS Usman Yusuf

Najeriya
Image caption Majalisar Wakilai ta ce korar Dr Yusuf za ta kawo cikas kan binciken da take gudanarwa

'Yan Majalisar Wakilan Najeriya sun bukaci ministan lafiya na kasar da ya mayar da Shugaban Hukumar Insorar Lafiya (NHIS), Dr Usman Yusuf, kan mukaminsa bayan da aka dakatar da shi bisa zargin cin hanci da rashawa.

Dambarwa ta taso ne a cikin makon jiya, lokacin da Ministan Lafiyar kasar, Farfesa Isaac Adewole ya dakatar da shugaban hukumar bayan an zarge shi da aika wasu laifuka da ke da alaka da cin hanci da rashawa, batun da ya musanta.

Sai dai kwamitin na kallon wannan mataki a matsayin wani bi-ta-da-kulli kan bayanan da babban sakataren ya gabatar a yayin wani zaman sauraron ra'ayin jama'a da kwamitin lafiya na Majalisar Wakilan ya gudanar watan jiya.

Mataimakin shugaban kwamitin lafiya a majalisar wakila, Honourable Muhammad Usman ya shaida wa wakilin BBC cewa, biyu daga cikin abubuwa uku da suka roka kuma majalisar ta amince da su sun hada da cewar kada a ci gaba da yin sabuwar rijistar har sai kwamitin ya kammala bincikensa.

A watan Nuwamban bara ne majalisa ta umarci a yi bincike a fannin insorar lafiyar, amma har yanzu an ce ana cigaba da samun matsaloli.

Dan majalisar ya kara da cewa mara lafiya ba sa samun kulawa kamar yadda ya kamata.

A jawabin da ya gabatarwa kwamitin majalisar, Farfesa Umar Yusuf, ya ba da misalin cewa ya sa hannu kan sama da biliyan 60 kuma an bai wa dillalan inshorar, amma mutane ba sa amfana kuma an saka sunayen bogi na sama da 23,000 da ake amfani da su wajen fitar da kudade.

Sai dai kwamnitin ya bayyana cewa akwai abubuwa da dama suka hanasu gudanar da binciken a baya.

Kuma an dakatar da sakataren hukumar ne a dai-dai lokacin da suka fara bincike, a don haka suna ganin wata hanya ce ta hana shi bada bayanai kan irin makudan kudaden da ake sace wa 'yan Najeriya.

Labarai masu alaka