Karar injin jirgi ta kashe wata mata a New Zealand

Mutane na iya kallon jirgi kasa-kasa a duk lokacin da zai tashi ko sauka Hakkin mallakar hoto Princess Juliana Airport
Image caption Mutane na iya kallon jirgi kasa-kasa a duk lokacin da zai tashi ko sauka

Wata 'yar kasar New Zealand ta mutu a tsibirin Sint Maarten da ke yankin Karibiyan, sakamakon karfin iskar injin jirgin sama a lokacin da yake tashi, wanda yajefar da ita a kasa warwas.

Lamarin ya faru ne a shahararren filin jirgin saman nan mai suna Princess Juliana, wanda ba shi da nisa sosai daga bakin teku.

Masu zuwa shan iska a bakin tekun za su iya tattaki zuwa katangar filin jirgin a duk lokacin da jirgi ke tashi.

'Yan sanda sun ce matar mai shekara 57 tana tsaye ne a jikin katangar filin jirgin kafin karfin injin jirgin a dalilin tashin da ya yi ya wurgar da ita, lamarin da ya sa ta ji mummunan rauni.

An kai ta asibiti domin ba ta kulawa, amman ta mutu daga baya.

Hakkin mallakar hoto BBC/Google

Alamun hatsari

Gabar tekun da lamarin ya faru wuri ne da masu yawon bude ido suke so domin ana iya ganin jirage a kasa-kasa yayin sauka da tashin su.

Farkon titin jirgin saman na da nisan mita 50 ne kawai daga katangar da ke bakin teku mai suna Maho beach, kuma yana da irin wannan nisan daga bakin ruwa.

Akwai manyan alamu na gargadi da ke umurtar masu zuwa wurin cewar ka da su tsaya a kusa katangar.

Duk da hatsarin, wasu faya-fayen bidiyo da ke yawo a Intanet sun nuna masu yawon bude ido suna rike da katanagar gam-gam domin ka da ruwa ya tafi da su - a wasu lokutan ma ruwan na kusan tafiya da su.

Karin bayani