Cameroon: 'Yan kunar bakin wake sun kashe mutum 12

Boko haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kimanin mutum 40 ne suka jikkata kuma galibinsu munanan raunuka ne

Kimanin mutum 12 ne suka rasa rayukansu bayan harin kunar bakin wake a garin Wara na kan iyakar Najeriya da Kamaru.

An kai harin ne a ranar Laraba a wani wuri mai cike da hada-hadar jama'a.

Kimanin mutum 40 ne suka jikkata kuma galibinsu munanan raunuka ne.

Ko da yake, babu wanda ya dauki alhakin kai harin tukunna, amma ana ganin harin ya yi kama da irin wanda kungiyar Boko Haram take kai wa a yankin.

A watan jiya ma an kai hare-hare biyu a arewacin Kamaru, kuma kusan ko wanne mako ana samun harin kunar bakin wake a iyakar kasar da Najeriya.

Har ila yau, a ranar Talata 'yan kunar bakin wake hudu ne suka kai hari a Jami'ar Maiduguri a arewacin Najeriya inda a kalla mutum 12 suka rasa rayukansu.

Labarai masu alaka