'Malamai na koyawa dalibai akidun al-Shabab'

Kungiyar al-Shabab na son baza akidarta a mkarantun Somaliya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar al-Shabab na son baza akidarta a mkarantun Somaliya

Hukumomin Somaliya sun kama wasu malaman makaranta bakwai kan zargin su da yin wata ganawa da mayakan al-Shabab.

An ce malaman sun hadu ne don tattaunawa kan sauya manhajar karatun makarantu masu zaman kansu, ta yadda zai yi daidai da akidar kungiyar al-Shabab masu tsaurin ra'ayin addini.

Ko wanne daya daga cikin malaman makarantar, wadanda suka kasance shugabannin makarantun ne, zai dauki nauyin dalibai wajen 1,000, masu shekaru daga bakwai zuwa 15.

Tun kusan shekara 10 da ta gabata kungiyar al-Shabab ke kokarin jangwalo yaki da gwamnatin Somaliya.

Mahad Hassan Osman, ministan yada labarai na yankin Hir-Shabelle a Somaliya ya gayawa BBC cewa, 'an kama malaman ne a kusa da garin Jowhar.'

"Mun kama su daga nisan kilometer 15 daga gari. Suna kokarin sauya manhajar karatun makarantun ne yadda zai dace da abun da 'yan kungiyar al-Shabab suka yarda da shi na tsaurin ra'ayin Islama."

Ministan ya ce za a kai malaman kotu bayan an gama gudanar da bincike a kansu.

Al-shabab tana da alaka da kungiyar Al-qaeda. An kore su daga cikin garuruwan Somalia amma har yanzu suna da iko a wasu kauyukan da dama.

A watan Afrilu ne kungiyar ta kaddamar da manhajar karatunta da salon yadda za a dinga koyarwa, da kuma wallafa littatafan karatu masu koyar da tsaurin ra'ayi.

An harbe matashin ministan gwamnatin Somalia

Yara Amurkawa 1,300 ne ke mutuwa ta hanyar harbin bindiga

Labarai masu alaka