Mutane sun kashe dorinar ruwa 27 a Niger

Dorinar Ruwa Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mazauna wani kauye a yammacin Niger sun kashe dorinar ruwa fiye da 27 saboda suna zargin su da lalata musu shuka da cutar musu da dabbobi.

Mai garin yankin Ayorou Jando Rhichi Algaher, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, mutane sun fara yi wa dabbobin kisan kiyashin ne a watan Maris, daga bisani sai al'amarin ya ta'azzara musamman a kauyukan da ke kusa da kogin Niger.

Ya kara da cewa an kama mutum goma sakamakon kashe dorinar ruwan, amma tuni an saki wasu daga cikin su.

A watan Mayu, sarakunan gargajiya sun yi kashedi a kan dorinar ruwan, inda suka ce sune suke yin barna ga shukoki da kuma yin barazana ga jiragen ruwan da suke kogin Niger.