Nigeria: Kotu ta bayar da belin Saminu Turaki

Saminu Turaki Hakkin mallakar hoto Saminu Truaki Facebook
Image caption Gwamnan zai rika kai kansa ofishin hukumar EFCC duk bayan mako biyu

Wata kotu a Najeriya ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Saminu Turaki bayan hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta'annati (EFCC) ta kama shi bisa zargin wawure naira biliyan 36 a lokacin da yake kan mulkin jihar.

An bayar da belinsa ne bayan wasu mutum biyu mazauna Abuja sun tsaya masa.

Har ila yau, kotun ta bukaci tsohon gwamnan ya rika kai kansa ofishin hukumar EFCC duk bayan mako biyu.

Hakazalika, kotun ta dage zamanta har sai ranar 20 ga watan Yulin shekarar 2017.

Saminu Turaki, wanda ya yi mulkin jihar Jigawa na tsawon shekara takwas wato tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.

Labarai masu alaka