Kotu ta ci tarar lauyan Evans

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Evans ya yi karar rundunar 'yan sandan Najeriya ne bisa zargin suna tsare shi ba bisa ka'ida ba

Wata babbar kotu a Najeriya ta ci tarar lauyan madugun da ake zargi da satar mutane wato Evans naira 20,000.

Alkalin kotun wadda take a jihar Legas Mai shari'a Abdulazeez Anka ya gargadi lauya Olukoya Ogungbeje kan ya guji aikata abin da ya saba wa aikinsa na lauya.

Chukwuduneme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, ya shigar da kara ne a gaban kotun inda ya ce ana tsare da shi ne ba bisa ka'ida ba, don haka yake bukatar a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Hakazalika ya ce idan kuma babu wata tuhuma a kansa, "to yana bukatar a sallame shi ba tare da bata lokaci ba."

Evans ya maka 'yan sanda a kotu

Evans ya so ya gagari jami'an tsaron Nigeria – Abba Kyari

Evans yana nan bai gudu ba – 'Yan sandan Nigeria

A watan jiya ne Evans ta hannun lauyansa ya shigar da rundunar 'yan sandan kara a gaban wata babbar kotun kasar, inda yake zarginsu da tsare shi ba bisa ka'ida ba.

An cafke Evans ne a farkon watan Yuni a Legas tare da wasu mutum shida da ake zarginsu da satar mutane.

Labarai masu alaka