Hira da Adam A. Zango
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An hana ni aure saboda zargin luwadi – Adam A Zango

  • Akwai sautin cikakkiyar hirar da BBC ta yi da jarumin, sai ku latsa alamar lasifika da ke saman hotansa don sauraro.

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A Zango, ya ce a kullum yana kwana yana tashi da bakin cikin zargin da wasu suke yi masa na zama dan luwadi (neman maza).

A wata hira ta musamman da BBC, Zango ya ce wannan ne ya sa a wani lokaci a baya jarumin ya dauki Alkur'ani ya rantse cewa bai taba neman wani namiji da lalata ba.

"Wannan abin yana hana ni barci, kai har ma na taba zuwa neman aure amma aka hana ni saboda haka," in ji Zango.

Game da batun cewa dan wasan yana da girman kai, jarumin ya kare kansa "Idan kana maganar masoya kana maganar miliyoyin mutane, to ta ya ya zan gamsar da su?"

Daga nan ya nemi masoyansa su rika yi masa uzuri domin shi ma mutum ne kamar kowa, kamar yadda ya ce.

A karshe ya yi magana kan yadda ake cewa 'yan wasan Hausa "kudi suke nema kawai", inda ya ce "muna yin fina-finan da za su kawo mana kudi."

Adam Zango ya kuma tattauna abubuwa da dama a hirar ciki har da alakarsa da Ali Nuhu da Nafisa Abdullahi da sauran batutuwa.

Labarai masu alaka