'Akwai hannun gwamnatin jihar Taraba a kisan Fulani'

Rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma ya zama ruwan dare a arewacin Najeriya
Image caption Fulani dai na fama da tashe-tashen hankali da sauran kabilu

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah da ke Najeriya ta shirya shigar da kara a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC da ke Hague, mako mai zuwa.

Kungiyar ta Fulani dai ta yi zargin cewa an yi wa al'ummar Fulanin kisan kiyashi a Mambila da ke karamar hukumar Sardauna a jihar Taraba.

A 'yan makonnin da suka gabata ne dai aka yi ta samun rikici mai nasaba da kabilanci tsakanin Fulani da Mambilawa.

Alkaluman da ba na gwamnati ba sun nuna mutane kimanin dubu daya sun mutu sannan an kashe dabbobi fiye da dubu uku.

Kungiyar ta GanAllah ta ce tana zargin gwamnatin jihar da hannu a cikin rikicin.

To sai da kwamishinan yada labarin jihar Taraba, Anthony Danburam ya musanta duka zarge-zargen, yana mai cewa babu hannunsu a ciki.

Lauyan da zai jagoranci gabatar da karar a kotun ta duniya,Farfesa Yusuf Dankofa ya shaida wa BBC cewa suna da shaidar cewa gwamnan jihar da kakakin majalisar sun yi kalaman da suka tunzura mutane.

Hassan Ahmed ya kuma kara da cewa ba su gamsu da matakan da gwamnatin jihar Taraba ke dauka domin dakile rikicin.

Sannan kuma kwamitin da jihar ta kafa ba ta tunanin za ta yi wa Fulani adalci saboda babu wakilcin Fulanin a kwamitin.

Rikici tsakanin makiyaya da manoma dai a jihar Taraba ya dade yana ruruwa.

Sai dai kungiyar GanAllah ta Fulani ta ce kisa ne irin na kiyashi ake shiryawa domin kawar da Fulani da dabbobinsu.