'Ba ma jin dadin yadda damisa ke neman karewa a duniya'

Akwai damisa 2,200 a India Hakkin mallakar hoto China News Service
Image caption Damisa na wasa a junansu

Masu rajin kare dabbobin gida daga nau'in azabtarwa da kisa sun zargin hukumomi a India bisa gazawa wajen hana yawaitar kisan damisa.

A kalla damisa 67 ce ta mutu a India a wannan shekarar, sai dai kuma masu fafutukar kare dabbobin sun ce ba kasafai ake iya fahimtar dalilin da ya sa suke mutuwar ba.

Su kan danganta mutuwar dabbobin da ikon Allah da kuma sakamakon karuwar sare da kone dazukan da damisar ke samun walwala a ciki.

Suna ganin yawan ido biyu da damisa ke yi da masu yawon bude ido ne ke sa su rashin shakkar masu farautarsu.

Sai dai kuma duk cewa damisa na mutuwa a India amma yawanta karuwa yake yi, a inda a yanzu haka akwai damisa 2,200 idan aka kwatanta da 1,500 a farkon wannan karni.