Rwanda ta kashe masu satar rake da ayaba

Rwanda Hakkin mallakar hoto HUMAN RIGHTS WATCH
Image caption Wasu daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin daurin rai da rai

Human Rights Watch ta ce hukumomin Rwanda sun zartar da hukuncin kisa a kan mutum 37 kan aikata ƙananan laifuffuka, ba tare da ba su damar daukaka kara ba.

Amma gwamnatin Rwanda ta musanta zargin da cewa kisan bai faru ba.

Mafi yawa daga cikin mutanen ana zargisu da laifin sata ne, daya daga cikin su laifin satar ayaba aka same shi da yi, sai kuma wani da ya saci rake.

Wasu kuma an zargesu da fasakwaurin tabar wiwi, da shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba, da kuma kamun kifi ta haramtacciyar hanya.

Human Rights Watch ta ce an yankewa mutanen hukuncin kisa tsakanin watan Yuli bara, zuwa watan Maris din shekarar nan, a yammacin kasar Rwanda.

Ta ƙara da cewa sun yi amanna, wannan na cikin dabarar cusa tsoro a zukatan jama'a, da tilasta su bin doka, da kuma hana mutane nuna taurin kai ga manufofin gwamnati.

Shaidu sun shaidawa ƙungiyar cewa, an yankewa wani mutum da ake zarginsa da satar saniya hukunci a bainar jama'a.

Ministan shari'a na Rwandan, Johnston Busingye ya mayar da martani akan shafinsa na tweeter da cewa rahoton ƙungiyar ƙarya ne, a ra'ayinsa Human Rights Watch na son hankalin jama'a ya dawo kan ta ne.

A baya dai, Ƙungiyar, ta zargi gwamnatin Rwanda da kai dubban yara da mata masu zaman kansu haramtattun cibiyoyin tsare mutane, zargin da gwamnati ta musunta.HRW ta zargi gwamnatin Rwanda da hallaka mutane