Sauya sunan Etsalat 'ba zai shafi abokan hulda ba'

Etisalat
Image caption Kamfanin Etisalat Nigeria na hadin gwiwa ne da takwaransa na hadaddiyar daular larabawa mai hedikwata a birnin Abu-Dhabi

A Najeriya kamfanin sadarwa na Etisalat ya ce janyewar da abokan hadin-gwiwarsa na Abu-Dhabi suka yi, da kuma yunkurin sauya sunan kamfanin ba za su shafi ayyukansa ba.

Duk da cewa kamfanin bai tabbatar da haban a hukumance ba, amma rahotanni sun ce an sauya masa suna daga Etisalat zuwa 9Mobile.

Masu amfani da layin Etisalat, da dama dai na fargabar mokamarsa, sakamakon rikicin biyan bashin fiye da dala biliyon daya da bankuna ke bin kamfanin.

To amma kuma manajan cinikin kamfanin a shiyyar arewacin Najeriya Mallam Babangida Mukaddas ya ce kowa ya kwantar da hankalin sa, babu wani abu da zai shafi huldar su da abokan kasuwanci, haka kuma ya ce akwai matakan da za su dauka dan raya kamfanin.

Ya kara da cewa daman kamfanin na hadin gwiwa ne tsakanin Najeriya da gwamnatin Abu-Dhabi, matsin tattalin arziki da tahin dalar Amurka da koma bayan tattalin arziki da Najeriya ta samu kan ta a ciki shi ne ya rubanya kudin bashin da ake bin kasar.

Mahukunta sun shiga tsakani an kuma kafa kwamitin yadda za a ci gaba da gudanar da kamfanin, ma'aikatan kanfanin za su ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Sannan jita-jitar da ake yadawa cewa za a rufe kamfanin Etisalat ba gaskiya ba ne, sauya suna kadai ake tunanin za a yi amma dai har yanzu ba kammala tattaunawa ba.

Babu abinda zai shafi ma'aikata, ko abokan hulda, ko yanayin kudin da kamfanin ke cajar abokan huldar sa.

Babangida Mukaddas ya kara nana ta cewa ''Ba za a rufe kamfanin Etisalat ba, ba kuma za mu sallami ma'aikata ba, hulda tsakanin mu da musu amfani da layin ta na nan daram sai ma fatan kara inganta ta''.

Labarai masu alaka