'An kashe 'yan Nigeria 97 a Cameroon'

Buhari and Biya
Image caption Kamaru da Najeriya na cikin sojin kawance na yakan kungiyar Boko Haram

Wasu 'yan Najeriya sun ce ana gallaza musu kuma an kashen 'yan Najeriya 97 a yankin Bakassi da ya koma hannun Kamaru daga Najeriya.

'Yan Najeriyan da suka arce daga yakin Bakassin sun yi zargin cewar jandarmomi na bin gida-gida domin karbar kudaden haraji, wanda suka ce ana tsawwala musu kuma sukan harbe wadanda suke nuna musu turjiya.

A nata bangaren, gwamnatin Najeriya ta ce rahoton gallazawa 'yan kasar a Kamaru ya saba wa yarjejeniyar da kasashen biyu suka rattaba wa hannu a shekarar 2005, lokacin da Najeriya ta mika wa Kamaru ikon yankin na Bakassi.

'Yarjejeniyar ta ba duk dan Najeriyar da ke da bukatar zama a can, na iya yin haka ba tare da an musguna musu ba.

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta bukaci jakadan Kamaru ya yi mata bayani game da rahotannin cin zarafin 'yan Najeriyan, kuma ta umurci ofisoshin jakadancin ta da ke biranen Yaounde da Boa da su binciki rahotannin domin tantance gaskiyar abin da ya faru.

Bugu da kari, ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Abdulrahman Dambazau, ya shaida wa BBC cewar shi da takwaransa na harkokin waje na shirin nika gari zuwa kasar ta kamaru bayan samun bayani daga gwamnan jihar Kurosriba, inda daruruwan wadanda suka gudo daga yankin na Bakassi ke fakewa.

Minista Dambazau ya ce ba ya ga hakan, tawagar tasu za ta nemi sanin gasiyar rahotannin da ke cewa ana musgunawa 'yan Najeriya da ke gudun hijira a Kamaru.

Wakilin BBC, Haruna Shehu Tangaza, ya ce duk da cewar mahukuntan Kamaru ba su mayar da martani ba game zargin musgunawa 'yan Najeriya, a shekara ta 2009 Kamaru ta ce ta rasa 'yan kasarta 21 ciki har da sojoji.

Kamarun ta yi zargin wasu gungun masu aikata laifuka daga Najeriya ne suka kai musu harin a yankin na Bakassi.

Ga rahoton Haruna Shehu Tangaza:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
"Ana gallaza wa 'yan Najeriya a Kamaru"

Majalisar Najeriya ta Dau Mataki:

Majalisar wakilan Najeriya ta ce za ta binciki zargin da ake yi na kashe 'yan Najeriya 97 a yankin na Bakassi da ya koma karkashin ikon Kamaru.

Majalisr ta yanke shawarar ne ranar Juma'a bayan zazzafar muhawarar da aka tafka game da rahotannin zarge-zargen musguna wa 'yan Najeriyar da ke zama a yankin.

'Yan majalisar sun ce wannan musguna wa 'yan Najeriyar ya saba wa yarjejeniyar Green Tea da kasashen suka rattaba wa hannu a shekarar 2005 lokacin da Najeriya ta mika wa Kamaru Bakassi.

Labarai masu alaka