Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya

Wasu daga cikin kyawawan hotuna daga nahiyar Afirka da kuma na 'yan Afirka dake zaune a wasu sassan duniya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption "Messengers of the Ancestors " na gudanar da ayyukan bauta a wajen birnin Kinshasa, babban birnin kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jagoran kungiyar Koko Lunda Kamosi yana nuna kundin rubutun da aka yi cikin harshen Nati-Kongo wanda yake da haruffa 23. Shugabannin addinin sun ce suna kira ne don dawo da ainihin addinin bakaken fata tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka da kuma addinin Kirista
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wasu 'yan Laberiya suna daukar hoton wani malamin addinin Musulunci wanda yake zaune a Amurka da yake yi musu jawabi a cikin filin wasan kwallon kafa da ke Monrovia ranar Lahadi.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sheikh Ahmed Mohammed Awal ya ziyarci kasar laberiya, tsohuwar kasar da ake cinikin bayi, a wani yunkurinsa na fadada kira zuwa addinin Musulunci
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mai tallan kayan ado yayin da ake mai kwalliya a Koriya ta Kudu, gabannin daukansa a hoto a birnin Seoul, Han Hyun-Min, wanda mahaifinsa dan Najeriya ne, tauraruwarsa ta na haskawa a kasar, duk da wariyar launin fata da masu ruwa biyu suke fuskanta , inda ake kiransu da sunan "Mongrels".
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani ma'aikaci a ma'aikatar sufurin jiragen saman kasar Ivory Coast wanda ke duba karfin wutar lantarkin kasashen Afirka ta yamma ranar Litinin, wanda zai kula da karfin wutar lantarkin kasashen Afirka ta yamma. Aikin na daga cikin ayyunkan da ma'aikatar sufurin jiragen sama ke yi da niyyar don samun saukin gano layukan wutar lantarkin dake bukatar gyara.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu 'yan kasar Tunisiya ke nan, yayin kammala wasan Super Nintendo Console na biyu a kasar ranar Lahadi a garin Le Kram, dake arewacin babban birnin kasar
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wadansu mutane da suka halarci gangamin siyasa a birnin Nairobi ranar Juma'a, yayin da suke nuna goyon bayansu ga jam'iyyar adawa ta Orange Democratic Movement , a babban zabe na 8 ga watan Agusta mai zuwa.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wadansu matasa suna nuna wani rubutu da yake nuna sakon zaman lafiya, a wani gangamin addu'a da aka yi wa Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta a Nairobi ranar Juma'a.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon fitaccen mawakin Uganda, Robert Kyagulani, wanda aka fi sani da Bobi Wine, yana annashuwa bayan da ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin dan majalisa a ranar Juma'a, bayan nasarar da ya samu a zaben cike gibin da aka yi, a matsayin dan takarar Indifenda a zaben watan da ya gabata. Tsohon mawakin ya sha alwashin kare hakkin marasa galihi a majalisar kasar.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wadansu 'yan kasar Masar suna ninkaya tare da dawakansu a wani tafki da ke birnin Alkahira don guje zafin da ake yi ranar Laraba